An fara kada kuri’u a zaben ‘yan majalisun kasar Habasha
2021-06-21 20:26:58 CRI
Da safiyar yau Litinin ne miliyoyin ‘yan kasar Habasha, suka fita rumfunan zabe, domin kada kuri’un su a babban zaben ‘yan majalissun kasar karo na 6, inda ake sa ran za a zabi ‘yan majalisu 440 cikin jimillar kujerun ‘yan majalisun kasar 547,cikin sama da ‘yan takara 9,000 da za su fafata, kana za a zabi kansilolin yankuna.
A baya an dage kada kuri’un har karo biyu, kafin zaben na yanzu wanda zai gudana a yankunan jihohin kasar 7 cikin 10.
Kafin wannan karo, hukumar zaben kasar Habasha mai tsarawa da kula da zaben, ta yi gargaji game da yiwuwar fuskantar kalubalen tsaro da na tsare tsare, da kuma batun matsaloli masu nasaba da akwatunan zabe da magudun zabe, wanda a baya hakan ne ya tilasta mata dage zaben ‘yan majalisu sama da 107 cikin 547.
Al’ummar Habasha za ta zabi ‘yan majalisa cikin ‘yan takara daga jam’iyyu na hadin kan kasa da na yankuna 46, a gabar da ake hasashen jam’iyya mai mulki za ta samu gagarumin rinjaye.
A tsarin zaben Habasha, firaminista ne ke jagorantar gwamnati, kuma jam’iyyar dake da rinjayen kujeru a majalissar dokokin kasar ce ke fitar da firaminista, wanda ake rantsarwa bayan kammala kidayar kuri’u. (Saminu)