logo

HAUSA

Gwamnatin Habasha ta ayyana dakatar da bude wuta a yankin Tigray

2021-06-29 10:24:07 CRI

Gwamnatin Habasha ta ayyana dakatar da bude wuta a yankin Tigray_fororder_210629-Saminu2

Gwamnatin kasar Habasha ta ayyana dakatar da bude wuta a yankin Tigray mai fama da tashe-tashen hankula. Wata sanarwa da fadar gwamnatin ta fitar a jiya Litinin, ta ce za a aiwatar da matakan ba da agajin jin kai, da na kyautata rayuwar al’ummun yankin cikin lumana, a gabar da ayyukan noman damuna ke karatowa.

Tun daga ranar 4 ga watan Nuwambar bara ne dai sojojin Habasha, suka fara kaddamar da hare-hare kan dakarun ’yantar da Tigray ko TPLF a takaice, wadanda ke iko da jihar dake arewacin Habasha.  (Saminu)