logo

HAUSA

Shugaban NPP Na Ghana: Nasarar Yaki Da Talaucin Sin Ta Bayyana Kyakkyawan Shugabancin CPC

2021-06-06 17:30:07 CRI

Nasarar da kasar Sin ta samu a yaki da talauci ta bayyana kyakkyawan shugabancin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin CPC, shugaban jam’iyya mai mulkin kasar Ghana NPP, Frederick Worsemao Armah Blay ya bayyana haka a wata tattaunawarsa a kwanan nan da kamfanin dillancin labarai na Xinhua.

Da yake bayyana nasarar da kasar Sin ta samu wajen kawar da matsanancin talauci a matsayin wani al’amari mai ban mamaki da kasar mafi yawan al’umma a duniya ta cimma, shugaban jam’iyyar ya ce, “Wannan misali ne na kyakkyawan shugabanci, kuma ya kamata mu yi koyi daga wannan nasara."

Blay, wanda ya sha kaiwa ziyara zuwa kasar Sin a lokuta da dama, ya kara da cewa, abin da ya fi burge shi shi ne irin kokarin mahukuntan kasar wajen daidaita matsalolin rashin daidaiton ci gaba a tsakanin yankunan gabashin da yammacin kasar, da kuma bunkasa ci gaban muhimman fannoni a shiyyoyin yammacin kasar da suka hada da kayayyakin more rayuwa da ayyukan noma wanda hakan ya taimaka wajen cimma nasarar manufar kasar na kawar da talauci.

Ya ce, a bayyane take har yanzu kasashen Afrika da dama suna fama da matsalar koma bayan ci gaba duk da irin namijin kokarinsu, hakan ya kara bayyana muhimmancin karfafa hadin gwiwar Sin da Afrika a fannin yaki da talauci.

Blay ya yabawa kasar Sin bisa yadda take musayar nasarorin da ta samu. Ya ce, kasar Sin ta fahimci yadda za ta yi musayar ci gaba, ta fahimci yadda za ta taimakawa sauran kasashe, kana ta fahimci yadda za a samu ci gaba tare, kuma muna bukatar irin wannan hadin gwiwar.(Ahmad)

Ahmad