logo

HAUSA

Jirgin saman United Airlines ya dawo aiki a Ghana

2021-05-16 17:03:44 CRI

Kamfanin jiragen saman United Airlines a ranar Asabar ya sake kaddamar da ci gaba da aikin jigilar fasinja tsakanin birnin Washington, D.C. na kasar Amurka zuwa Accra, babban birnin kasar Ghana, bayan dakatar da ayyukansa kusan shekaru goma da suka gabata.

Jawabin da aka karanta a madadin ministan sufurin kasar Kweku Ofori Asiamah, a taron manema labarai a filin jiragen saman kasa da kasa na Kotoka, an yaba wa matakin da kamfanin jiragen saman na United Airlines ya dauka na sake kaddamar da ayyukan sufuri daga birnin Washington, D.C. a ranakun Litinin, Alhamis, da Asabar, kuma ana fatan sannu a hankali zirga-zirgar za ta karu zuwa ta ko wace rana.

Jirgin saman United Airlines ya fara zuwa kasar Ghana ne a ranar 21 ga watan Yunin shekarar 2010, sannan ya fice daga kasar bayan shafe shekaru biyu yana aiki a watan Yulin shekarar 2012.

Ministan ya ce, ko da yake annobar COVID-19 ta haifar da mummunan koma baya ga kamfanonin jiragen saman kasa da kasa, sai dai fara amfani da riga-kafi ya baiwa kasar Ghana fata wajen samun farfadowa.

Ya kara da cewa, ana fatan gwamnatin Ghana ta hanyar ma’aikatar sufurin kasar za ta baiwa dukkan masu ruwa da tsaki goyon baya da taimakon da suke bukata wanda ya shafi amfani da ‘yancin dan Adam na 5 wanda ya ba da ikon fadada ayyukan sufurin daga Accra domin cimma muradun gwamnatin kasar na tabbatar da Ghanan a matsayin cibiyar hada hadar sufurin jiragen sama ta yammacin Afrika.(Ahmad)

Ahmad