logo

HAUSA

Shugaban Ghana ya kaddamar da shirin bunkasa sashen hada fina-finai na kasar

2021-04-29 11:03:53 CRI

Shugaban Ghana ya kaddamar da shirin bunkasa sashen hada fina-finai na kasar_fororder_0429-ibrahim-1

A jiya ne, shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, ya kaddamar da wani shirin bunkasa sashen hada fina-finai na kasar.

A jawabinsa yayin kaddamar da shirin, shugaba Addo ya ce, tarihi, da al’adu,da wuraren muhallin halittu, da wasu abubuwa kamar sansani, da wuraren shakatawa na kasa, da wuraren na tarihi, da gandun daji, da shagulgulan da ake gudanarwa a fadin kasar, duk za a iya daukar hotunan bidiyonsu a kuma yi amfani da su a matsayin wuraren shakatawa..

Ya kuma bayyana fatan cewa, shirin da ake fatan zuba jarin da ya kai dala miliyan 25, zai taimaka wajen bunkasa tsarin hada fina-finan yanayin kasa, inda ake sa ran zai samar da guraben ayyukan yi kimanin 6,000, baya ga muhimmiyar gudummawa da zai bayar ga ci gaban kasar.(Ibrahim)

Ibrhaim