logo

HAUSA

Sin na fatan warware batun harbo jirgin fasinjan Ukraine cikin lumana

2020-01-13 19:51:35 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Geng Shuang, ya ce Sin ta yi bakin ciki da aukuwar hadarin jirgin saman kasar Ukraine, wanda kasar Iran ta harbo shi bisa kuskure.

Geng Shuang, wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da ya gudana a Litinin din nan, ya kara da cewa, Sin na fatan za a kai ga warware batun hadarin cikin lumana, tare kuma da kaucewa kara cukurkuda al'amarin.