Gwamnatin Iran ta amince da biyan diyyar fasinjojin jirgin saman Ukraine da aka harbo
2020-12-31 11:37:42 CRI
Gwamnatin kasar Iran, ta amince da biyan diyyar dalar Amurka 150,000 kan kowane fasinja, dake cikin jirgin saman kasar Ukraine da aka harbo, a sararin samaniyar kasar ta Iran, a watan Janairun shekarar nan mai karewa.
Kamfanin dillancin labarai na Iran ko IRNA a takaice, ya hakaito sashen shari’a na cibiyar gwamnatin Iran din na cewa, an umarci ma’aikatar hanyoyi da raya birane ta kasar, da ta tsara biyan diyyar dala 150,000, ko adadi daidai da hakan, ga iyalan mutanen dake cikin jirgin ba tare da bata lokaci ba.
A cewar IRNA, diyyar ba ta kore batun bincike game da yiwuwar aikata laifi ba, game da harbo jirgin na kasar Ukraine.
A ranar 8 ga watan Janairun shekarar nan ta 2020 ne aka harbo jirgin saman kasar Ukraine, da wani makami mai linzami, jim kadan bayan tashin sa daga filin jirgin saman birnin Tehran, lamarin da ya sabbaba rasuwar daukacin mutane 176 dake cikin jirgin. Daga bisani, mahukuntan Iran sun tabbatar da cewa, dakarun tsaron kasar ne suka harbo jirgin bisa kuskure. (Saminu)
Labarai Masu Nasaba
- Iran ta yi kira da dakarun sojin ketare da su fice daga yankunanta
- Iran ta kara yawan sunayen Amurkawan da take zargi da hannu a kashe Soleimani zuwa 48
- Kasar Sin ta bukaci a yi kokarin mayar da yarjejeniyar nukiliyar Iran bisa turba
- Kasar Sin ta yi kira ga Amurka ta gaggauta komawa yarjejeniyar nukiliyar Iran