Ukraine ta sanar da soke sa hannu kan sanarwar hadin gwiwa na adawa da Sin
2021-06-27 11:20:24 CRI
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Ukraine ta bayar da sanarwa a daren ranar 24 ga wata, inda ta jaddada cewa, Ukraine ta dora muhimmanci ga dangantakar abokantaka dake tsakaninta da kasar Sin, kana a ranar 25 ga wata, ta sanar da soke sa hannu kan hadaddiyar sanarwar da tsirarrun kasashenyammacin duniya suka bayar kan yanayin hakkin dan Adam na Xinjiang na kasar Sin.
An bayar da sanarwa a shafin yanar gizo na tawagar wakilan kasar Ukraine dake Geneva cewa, kasar Ukraine ta riga ta soke sa hannu kan hadaddiyar sanarwar yanayin hakkin dan Adam na Xinjiang na kasar Sin da aka bayar a yayin taron karo na 47 na kwamitin hakkin dan Adam na MDD a ranar 22 ga wata.
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Ukraine ta bayar da sanarwa a daren ranar 24 ga wata, inda ta jaddada dora muhimmanci kan dangantakar abokantaka dake tsakaninta da Sin, da daina tsoma baki kan harkokin cikin gida na kasar Sin. Kana ta bayyana aniyarta ta ci gaba da sa kaimi ga raya dangantakar dake tsakaninta da Sin bisa ka’idojin nuna girmamawa ga juna kan kiyaye ‘yancin kai, da ikon mulkin kasa, da kuma cikakkun yankunan kasa. (Zainab)