logo

HAUSA

Wang Yi ya gayyaci jakadun kasashe fiye da 100 don ziyartar cibiyar tarihin JKS

2021-06-24 15:28:04 CRI

Wang Yi ya gayyaci jakadun kasashe fiye da 100 don ziyartar cibiyar tarihin JKS_fororder_210624-Ahmad5

Da safiyar yau Alhamis 24 ga watan Yuni, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya gayyaci jakadun kasashen waje da wakilan kungiyoyin kasa da kasa da ke nan kaar Sin da su ziyarci cibiyar adana kayan tarihin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin JKS.

Sama da jakadun kasashen waje 100 da wakilan kungiyoyin kasa da kasa ne suka ziyarci cibiyar tarihin. Jakadun sun taya murnar cika shekaru 100 da kafuwar JKS, sun yabawa manyan nasarori masu ban mamaki da aka cimma karkashin jagorancin jam’iyyar ta JKS, kana sun bayyana aniyarsu na karfafa hadin gwiwa da cudanya da jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin da kuma kara zurfafa huldar dake tsakaninsu da kasar Sin. (Ahmad)