logo

HAUSA

JKS ya sha yabo daga sassan kasa da kasa yayin da yake cika shekaru 100 da kafuwa

2021-06-24 17:08:28 cri

JKS ya sha yabo daga sassan kasa da kasa yayin da yake cika shekaru 100 da kafuwa_fororder_1

Yayin da jam’iyyar Kwaminis mai mulkin kasar Sin ke cika shekaru 100 da kafuwa, sassan shugabannin kasashen duniya, da masana, da masu fashin baki, na ci gaba da jinjinawa manyan nasarorin da jam’iyyar ta samu, tare da bayyana fatan alheri ga makomarta a nan gaba.

Shugabannin kasashen duniya da dama, sun nuna matukar gamsuwa da irin tasirin da JKS ta haifar ga ci gaban kasar Sin, musamman ma irin rawar da ta taka wajen tsame miliyoyin al’ummar Sinawa daga kangin talauci cikin kusan shekaru 40.

Masharhanta a nasu bangare kuwa, na ta bayyana mamaki game da irin nasarar da wannan jam’iyya ta samu cikin shekaru kalilan. Irin ci gaban da baya ga alfanun da ya haifar ga ita kan ta kasar Sin, ya kuma ba da wata muhimmiyar gudummawa ga ci gaban duniya baki daya, musamman a fannin tallafawa yaki da talauci, da ingiza ci gaban tattalin arziki da sauran su.

Ko shakka babu, JKS ta zamo “Zakaran Gwajin Dafi”, a fannin raya kasa, inda akidunta na markisanci, da matakan raya kasa na gurguzu masu halayyar musamman na kasar, suka zamo abun misali ga dukkanin kasashen duniya, a fannin samar da ci gaba ta hanyar sanya rayuwar al’umma gaban komai, da raba gajiya cikin daidaito, da kuma samar da jagoranci na gari.

Bugu da kari, JKS ta dinke kan daukacin al’ummun Sinawa, wanda hakan ya sanya ta zama mai cikakkiyar karbuwa tsakanin ’yan kasar, kuma da yake Bahaushe kan ce “Na Gari Na Kowa”, JKS ta samu karbuwa hatta ma ga sauran kasashe dake shaida irin nasarar da ta cimma, cikin wadannan shekaru 100.

Ko shakka babu, JKS ta taka rawar gani wajen shiga a dama da ita a harkokin kasa da kasa, ta kuma ba da tallafin wanzar da zaman lafiya da tsaro a duniya, ta kuma goyi bayan hadin gwiwar samar da ci gaba na bai daya, da cudanyar sassa daban daban, da nufin ganin an gudu tare an tsira tare.

Duniya ba za ta taba mantawa da gudummawar JKS ba, wajen ingiza manufar samar da al’ummar duniya mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil adama, da kwazon jam’iyyar na gabatar da shawarwari, da tunani mai amfani, don tunkara, tare da warware dunbin kalubale da duniya ke fuskanta. Tare da aza wani muhimmin tubali na gina kyakkyawar makoma mai inganci, wadda za ta tallafi ci gaban rayuwar daukacin bil adama a nan gaba! (Saminu Hassan)