logo

HAUSA

An gabatar da takardar bayani game da ayyukan JKS na girmamawa da tabbatar da hakkin dan Adam

2021-06-24 12:08:00 CRI

Ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gabatar da takardar bayani game da ayyukan Jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin na girmamawa da tabbatar da hakkin dan Adam a yau.

A cikin takardar, an yi nuni da cewa, a cikin shekaru 100 da suka gabata, jam’iyyar kwaminis ta Sin ta kiyaye maida hankali ga jama’a, da hadawa da ka’idojin kiyaye hakkin dan Adam da yanayin da ake ciki a kasar Sin, da maida ikon yin rayuwa da samun bunkasuwa a matsayin tushen hakkin dan Adam, da tabbatar da zaman rayuwar jama’a mai dadi, da sa kaimi ga dan Adam don ya samu bunkasuwa a dukkan fannoni, da kara baiwa jama’a jin dadi da tsaro a rayuwarsu, Sin ta kiyaye hanyar bunkasa hakkin dan Adam mai halayyar Sin ta musamman bisa tsarin gurguzu cikin nasara.

Takardar ta kara da cewa, a cikin shekaru 100 da suka gabata, JKS ta kiyaye taka hanyar samun bunkasuwa cikin lumana, da sa kaimi ga samun bunkasuwa tare. Sin ta kiyaye tabbatar da zaman lafiya a duniya, da sa kaimi ga samun ci gaba ta hanyar yin hadin gwiwa, da tabbatar da hakkin dan Adam ta hanyar samun ci gaba, da shiga harkokin kiyaye hakkin dan Adam na kasa da kasa, da samar da shirye-shiryen Sin kan ayyukan kula da hakkin dan Adam na duniya, haka kuma an sa kaimi ga raya sha’anin kiyaye hakkin dan Adam na duniya, da yin kokari tare da kasa da kasa wajen raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil’adama. (Zainab)