logo

HAUSA

Yadda JKS ta yi abin al’ajabi wajen kare hakkin dan Adama

2021-06-25 10:46:22 CRI

Yadda JKS ta yi abin al’ajabi wajen kare hakkin dan Adama_fororder_1

Jiya Alhamis 24 ga wata, ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya fitar da takardar bayani mai taken “Manyan ayyukan da jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ta yi, domin martaba da kare hakkin dan Adama”, inda aka ga namijin kokarin da jam’iyyar take yi wajen ingiza ci gaban sha’anin kare hakkin dan Adama a cikin shekaru 100 da suka gabata.

Daga takardar bayanin da aka fitar jiya, an ga irin kokarin da jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ta yi domin ciyar da sha’anin kare hakkin dan Adama a cikin shekaru 100 da suka gabata, haka kuma an ga yadda jam’iyya mai rike mulki a kasar Sin wato JKS ke zama tabbaci mafi muhimmanci yayin da ake ingiza ci gaban hakkin dan Adama a kasar ta Sin.

Yadda JKS ta yi abin al’ajabi wajen kare hakkin dan Adama_fororder_2

Kamar yadda aka bayyana a cikin takardar bayanin, abu mafi muhimmanci a cikin manufofin tafiyar da mulkin kasa na JKS, shi ne samar da rayuwa mai inganci ga jama’a, da farfado da al’ummar Sinawa. Tun bayan kafuwarta, jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin tana nacewa kan muradun hada ka’idojin kare hakkin dan Adama da hakikanin yanayin da kasar Sin ke ciki, kuma tana nacewa kan manufar mayar da hakkin rayuwa da hakkin bunkasa a gaban kome, haka kuma tana nacewa kan burinta na samar da rayuwa mai inganci ga al’ummar kasar, saboda tana ganin cewa, jin dadin rayuwa, shi ne hakkin dan Adama mafi muhimmanci ga jama’a, wannan ya sa jam’iyyar JKS ta yi nasarar kare hakkin dan Adama bisa tsarin gurguzu mai hallayar musamman ta kasar Sin.

An lura cewa, a fadin duniya, jam’iyyu masu rike mulki kalilan ne suke mai da hankali kan aikin kare hakkin dan Adama kamar yadda JKS take yi, hakika an rubuta kalaman “martaba da kuma tabbatar da hakkin dan Adama” a cikin ka’idojin JKS, kuma an rubuta kalaman a cikin kundin mulkin kasar Sin, har ma aikin kare hakkin dan Adama ya kasance wata muhimmiyar ka’ida yayin da mahukuntan kasar Sin suke gudanar da harkokin kasa.

A kasar Sin, “hakkin dan Adama” ba kalamam siyasa ne kawai ba, batu ne kowanen Sinawa yake iya ganin sakamakonsa da idanunsu, alal misali, karuwar kudin shiga, da shiga harkokin siyasa, da daidaiton ci gaban yankunan kasar, da wadatar yankunan mai kunshe da ‘yan kananan kabilu, duk wadannan sun alamta cewa, ci gaban kasar Sin da jin dadin rayuwar Sinawa ta nunawa al’ummun kasa da kasa babban sakamakon da kasar Sin ta samu wajen kare hakkin dan Adama.

Ana iya ganin wannan sakamakon daga aikin kawar da talauci a kasar, daga shekarar 2012, zuwa shekarar 2020, kasar Sin ta yi nasarar cimma burinta na fitar da al’ummunta dake rayuwa a kauyuka da yawansu ya kai miliyan 98 da dubu 990 daga kangin talauci bisa ma’auni na yanzu, a karkashin jagorancin JKS, lamarin da ya fito da wani sabon abin al’ajabi wajen kare hakkin dan Adama a fadin duniya, kuma ta cimma burin samun dauwamammen ci gaba nan da shekarar 2030 da MDD ta tsara, kafin shekaru goma, hakan ya sa gudummowar kasar Sin kan yaki da talauci a fadin duniya ta zarta kaso 70 bisa dari.

Kana an ga yada jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ta ba da muhimmanci kan batun lafiyar al’ummun Sinawa yayin da ake kokarin kandagarkin annobar cutar numfashi ta COVID-19, ta kuma dauki wajababbun matakai domin ceton kowanen mutum da ya harbu da cutar, lamarin da ya nuna cewa, JKS tana yin namijin kokari domin tabbatar da hakkin rayuwa da lafiyar jiki na al’ummun kasarta.

Daga kiyaye tunanin kare hakkin dan Adama, zuwa hakikanin ayyukan da JKS take dauka a bangaren, an lura cewa, kokarin da take yi ya samu yabo daga kasa da kasa, ya kuma amsa tambayar al’ummun kasa da kasa game da dalilin da ya sa JKS ta samu amincewa da goyon baya daga al’ummun Sinawa.

Babban sakataren jam’iyyar kwaminis ta kasar Afirka ta Kudu Blade Nzimande ya bayyana cewa, “Ko da yaushe JKS ta cimma matsaya guda daya da al’ummun Sinawa, tana yin kokari tare da su, kuma tana mai da hankali kan babbar moriyarsu, ta hanyar daidaita matsalolin da suka fi damunsu, wannan ya sa ta samu goyo baya da amincewa daga wajensu, har ta iya hada kai da al’ummun Sinawa yayin da take ciyar da kasar ta Sin gaba.”

A cikin shekaru 100 da suka gabata, JKS ta shaida ta hanyar daukar hakikanin matakai cewa, ita jam’iyya ce mai kishin zaman lafiya da ci gaba, wadda ke kokarin ingiza ci gaban sha’anin kare hakkin dan Adama na duniya.

Sakamakon da JKS ta samu bayan kokarin da take yi a cikin shekaru 100 da suka wuce, shi ma ya shaida cewa, bai dace kasashen yamma su bayar da ma’anar hakkin dan Adama ba, ya zama wajibi kowace kasa ta dauki matakin martaba da tabbatar da kuma bunkasa aikin kare hakkin dan Adama bisa hakikanin yanayin da take ciki.(Jamila)