logo

HAUSA

MDD ta yi kira da a himmantu wajen magance rashin daidaito yayin da ake kokarin kawo karshen cutar kanjamau a shekarar 2030

2021-05-01 16:30:17 CRI

Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya yi kira da a yi kokarin kawo karshen rashin daidaito domin dawo da duniya kan turbar fatattakar cutar kanjamau nan da 2030.

Antonio Guterres, ya ce an samu gaggarumar nasara wajen yaki da cutar a wasu wurare da kuma tsakanin wasu rukunoni, yayin da a wasu wurare na daban kuma, an bar annobar ta ci karenta babu babbaka, inda adadin mutanen da ta kashe ya yi ta karuwa.

A cewar wani rahoto da aka fitar jiya, sabbin mutane miliyan 1.7 da suka kamu da cutar a shekarar 2019 sun ninka har sau 3, kan mizanin da aka sanya na rage sabbin masu kamuwa da cutar zuwa kasa da 500,000 a shekarar 2020. Bugu da kari, adadin mutane 690,000 da suka mutu sanadiyyarta a shekarar 2019, ya zarce mizanin da aka sanya na shekarar 2020, na rage yawan adadin zuwa kasa da 500,000 a shekara. 

Sakatare Janar din ya bayar da shawarwari 10 da suka hada da ragewa da kawo karshen wariyar dake tsaiko ga kawo karshen cutar kanjamau da ba da muhimmanci ga matakan kariya da tabbatar da cewa, kawo shekarar 2025, kaso 95 na mutanen dake fuskantar barazanar kamuwa da cutar sun samu, tare da amfani da tarin damarmakin kariya, da cike gibin dake akwai wajen yin gwaji da samun kulawa da dakile yaduwarta daga uwa zuwa danta tare da kawo karshen kamuwar cutar a tsakanin yara.

Sauran shawarwarin sun hada da sanya daidaiton jinsu da kare hakkokin mata da ‘yan mata kan gaba cikin kokarin kawar da barazana da tasirin cutar, da cike gibin karancin kudin yaki da cutar da kara yawan kudin da ake zubawa na yaki da cutar a kasashe masu karanci da matsakaicin kudin shiga zuwa dala biliyan 29 nan da shekarar 2025. (Fa’iza Mustapha)

Fa’iza Mustapha