logo

HAUSA

Madam Peng Liyuan Ta Yi Jawabi A Taron WHO

2021-06-07 21:43:46 CRI

Madam Peng Liyuan Ta Yi Jawabi A Taron WHO_fororder_peng

Bisa gayyatar da aka yi mata, yau Litinin ne madam Peng Liyuan, mai dakin shugaban kasar Sin Xi Jinping, kuma jakadiyar sada zumunta ta hukumar kiwon lafiyar kasa da kasa kan rigakafin ciwon tarin fuka da cutar AIDS, ta yi jawabi a bikin bude taron WHO kan kara azama ga sa aya ga mutuwar masu fama da cutar AIDS sakamakon ciwon tarin fuka.

A cikin jawabinta, madam Peng ta ce, a shekarun baya, sakamakon kokarin da kasashen duniya suke yi tare, an samu kyakkyawan sakamako wajen rigakafin ciwon tarin fuka da cutar AIDS a duk duniya baki daya. Kana kasar Sin ta kafa tsarin hadin gwiwar hukumomi game da rigakafin ciwon tarin fuka da cutar AIDS sannu a hankali.

Kaza lika yawan masu kamuwa da cutar AIDS ba shi da yawa a kasar ta Sin. Kuma shekaru kusan 20 da suka wuce, yawan masu kamuwa da ciwon tarin fuka ya ragu da fiye da kaso 40 bisa dari, yayin da yawan mutuwar mutane sakamakon ciwon ya ragu fiye da kaso 70.

Peng ta kara da cewa, manyan cututtuka masu yaduwa, kalubale ne da daukacin ‘yan Adam suke fuskanta. Kuma kawar da ciwon tarin fuka da cutar AIDS, burinmu ne na bai daya. Yanzu haka cutar COVID-19 tana ci gaba da yaduwa a duniya, lamarin da ya kara haddasa barazana ga rigakafin ciwon tarin fuka da cutar AIDS. Don haka ake bukatar a yi kokari tare bisa kaunar juna. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan