logo

HAUSA

Taron WHA zai mayar da hankali kan yadda za a kawo karshen COVID-19 da yadda za a tunkari annoba a nan gaba

2021-05-25 10:38:47 CRI

Taron WHA zai mayar da hankali kan yadda za a kawo karshen COVID-19 da yadda za a tunkari annoba a nan gaba_fororder_WHA

Jiya ne aka bude babban taron lafiya na duniya (WHA), inda aka jaddada bukatar hanzarta kawo karshen annobar COVID-19 da ke ci gaba da addabar wasu sassan duniya, da ma yadda za a kimtsa tunkarar annoba da za ta iya bulla a nan gaba, ta hanyar gina tsarin ingantaccen tsarin kiwon lafiya, mai tsaro da kuma adalci a duniya.

Alkaluman hukumar lafiya ta duniya na nuna cewa, yau kusan sama da shekara guda, tun bayan bullar annobar COVID-19, yawan wadanda suka kamu da cutar, ya kai sama da miliyan 160, adadin da ya ninka sau sama da arba’in, yayin da cutar ta halaka sama da mutane miliyan 3, adadin da ya ninka sau 11.

Sai dai yayin da annobar ke ci gaba da yiwa kiwon lafiya da jin dadin jama’a barazana, ana saran taron na WHA na tsawon kwanaki 9 dake gudana a takar bidiyo, zai mayar da hankali kan yadda za a shirya, da ma tunkarar duk wata annoba da ka iya bulla a nan gaba.

A jawabinsa na bude taron, babban darektan hukumar lafiya ta duniya (WHO) Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya yi kira ga mambobin kasashe, da su yiwa a kalla kaso 10 cikin 100 na al’ummominsu riga kafi, nan da watan Satumban wannan shekara, da kuma a kalla kaso 30 cikin 100 nan da karshen wannan shekara, ma’ana a yiwa sama da mutane miliyan 250 dake kasashe masu karanci da matsakaicin kudaden shiga riga kafin cikin watanni hudu kacal.

Ya kuma bukaci kasashe, da su raba alluran riga kafin yanzu kuma cikin sauri ga shirin COVAX, wanda WHO ke jagoranta wajen ganin an raba alluran rigan kafin COVID-19 a fadin duniya cikin adalci.(Ibrahim)