logo

HAUSA

Me Ya Sa Amurka Ta Kau Da Kai Daga Yadda Ake Daukar Hayar Kananan Yara Su Yi Aiki A Amurka?

2021-06-11 21:06:14 CRI

Me Ya Sa Amurka Ta Kau Da Kai Daga Yadda Ake Daukar Hayar Kananan Yara Su Yi Aiki A Amurka?_fororder_amurka

A gabannin ranar 12 ga watan Yunin bana, wato ranar tabbatar da hana kwadagon kananan yara a duniya, hukumar ‘yan kwadago ta kasa da kasa ILO, da asusun kula da kananan yara na MDD, sun gabatar da rahoton cewa, a shekarar 2021, yawan kananan yara dake kwadago a duniya ya karu, a karo na farko cikin shekaru 20 da suka wuce.

Sa’an nan kuma, a yayin babban taron ‘yan kwadago na kasa da kasa karo na 109 da ake gudanarwa ta kafar bidiyo a Geneva, an sossoki yadda ake tilasta wa mutane su yi aiki, da kuma daukar hayar kananan yara don yin aiki a kasar Amurka. Wasu na ganin cewa, abubuwan da Amurka take yi sun tsananta matsalar daukar hayar kananan yara don yin aiki a duniya. Amurka ba za ta iya kau da kai daga wannan matsalar ba.

Jaridar The Washington Post ta Amurka, ta ruwaito cewa, daga shekarar 2003 zuwa 2016, kananan yara 452 ne a Amurka suka rasa rayukansu, sakamakon kwadago. To ko me ya sa ‘yan siyasar Amurka da suke kiran kansu masu rajin kare hakkin dan Adam, ba su ce komai kan lamarin ba? A shekarun baya da suka wuce, sau da yawa ILO ta nuna damuwarta, kan yadda ake daukar hayar kananan yara yin aiki a Amurka, tare da bukatar gwamnatin Amurka da ta daidaita batun tilastawa mutane yin aiki. Amma Amurka ta kau da kai daga batutuwan, har ma ta shafa wa kasar Sin kashin kaji. A cewarta ana tilastawa mutane yin aiki a jihar Xinjiang ta kasar Sin, a yunkurin dora wa kasar Sin laifi, da janyo hankalin kasashen duniya kan kasar Sin, ta yadda za ta bata sunan kasar Sin da danne kasar Sin.

Bata sunan wasu ba zai warware matsalolin da Amurka take fuskanta ba. Zai fi kyau irin wadannan ‘yan siyasan Amurka, su yi tunanin kiyaye hakkin dan Adam yadda ya kamata a kasarsu, da aiwatar da yarjejeniyar kula da harkokin ‘yan kwadago ta duniya, da warware matsalar tilasawa mutane yin aiki, da tabbatar da kiyaye halaltattun hakkokin Amurkawa. Su ma masu fafutukar kare hakkin dan Adam na Amurka, ya fi kyau su kare hakkin jama’arsu yadda ya kamata. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan