logo

HAUSA

Dole Ne Amurka Ta Dauki Matakin Ba Da Tallafin Rigakafi Nan Da Nan

2021-06-08 20:49:27 CRI

Dole Ne Amurka Ta Dauki Matakin Ba Da Tallafin Rigakafi Nan Da Nan_fororder_allura

Babban darektan hukumar lafiyar kasa da kasa wato WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya bayyana a wani taron manema labaru da aka gudanar a ranar 7 ga wata cewa, yanzu haka kasashe masu wadata sun yi wa al’ummunsu allurar rigakafin cutar COVID-19, da yawansu ya kai kusan kaso 44, bisa jimilar rigakafin da aka yi a duk duniya, amma adadin rigakafin da aka yi a kasashe masu karancin kudin shiga bai wuce kaso 0.4 bisa dari kacal ba.

Tedros Adhanom Ghebreyesus ya kara da cewa, wasu kasashe sun yi alkawarin samar da rigakafin. Don haka WHO na fatan cewa, za su cika alkawarinsu a watan Yuni da na Yulin bana.

Ko da yake ba a ambaci sunan kasashen ba, amma kowa na iya fahimtar kalaman Mr. Tedros. Domin kuwa a kwanan baya, gwamnatin kasar Amurka ta yi alkawarin tura rigakafin miliyan 80 zuwa ketare, kafin karshen watan Yunin bana. Amma ya zuwa yanzu, ba ta dauki hakikanin matakin yin hakan ba tukuna.

Wasu dai na tambayar cewa, ko dai kalaman siyasa ne na daban da Amurkan ta yi? Wato dai akwai shakku sosai game da alkawarin na Amurka. Har ila yau, gwamnatin Amurka da ta gabata, ta taba yin alkawarin samar wa kasar Sin da sauran kasashe masu tasowa tallafin kudi har dalar Amurka miliyan 100, domin yaki da annobar COVID-19, amma ya zuwa yanzu, ba ta bayar da ko da kwabo daya ba tukuna. 

A ‘yan kwanaki da dama da suka wuce, wasu kasashen yammacin duniya, sun gaza aikata abubuwan da suka bayyana za su yi, don gane da samarwa, da kuma rarraba rigakafin. Sun kare muradun kasashen su fiye da batun riga kafin COVID-19, lamarin da ya kawo cikas ga hadin gwiwar kasa da kasa, na yaki da annobar, wanda kuma kasashen duniya sun yi tir da hakan.

Ba da tallafin rigakafin COVID-19 ba batun siyasa ba ne, aiki ne na jin kai ga duniya. Kuma kowa na sane da cewa, kasar Sin tana ba da tata gudummowar a-zo-a-gani wajen yaki da annobar a duniya, in an kwatanta da Amurka, wadda ta sanya siyasa cikin batun tallafin rigakafin.

Ya zuwa yanzu, kasar Sin ta samar wa kasashe fiye da 80 masu tasowa, wadanda ke matukar bukatar rigakafin tallafi, tare da sayar wa kasashe fiye da 40 rigakafin. Jimilar rigakafin da kasar Sin take samarwa duniya ta wuce miliyan 350 baki daya. Kamar yadda jaridar Nanyang Business Daily ta kasar Malaysia ta bayyana, kasar Sin ta dauki hakikanin matakai, na tsaron lafiyar al’umma.  (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan