logo

HAUSA

Yang Jiechi Ya Tattauna Da Antony Blinken Ta Waya

2021-06-11 21:00:12 CRI

Yau Jumma’a, mamban hukumar siyasa ta kwamitin tsakiyar JKS, kuma darektan ofishin harkokin waje na kwamitin tsakiyar JKS Yang Jiechi, ya tattauna da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ta wayar tarho.

A cikin tattaunawarsu, Yang Jiechi ya ce, kasar Sin na himmantuwa wajen rungumar akidun kaucewa rikici, da fito na fito, tare da martaba juna da cimma gajiya tare, da maida hankali ga hadin gwiwa da Amurka, yayin da take tsayawa kan kiyaye ikon mulkin kai, da tsaron kasa, da moriyarta ta raya kasa.

Jami’in ya jaddada cewa, kamata ya yi Amurka ta daidaita batun keta hakkin dan Adam a gida, a maimakon tsoma baki cikin harkokin cikin gida na wasu kasashe bisa hujjar hakkin dan Adam. Yang Jiechi ya yi nuni da cewa, kasar Sin na goyon baya, da shiga ayyukan hadin gwiwar kasa da kasa ta fuskar yaki da annobar COVID-19 cikin himma da kwazo. Kaza lika ba za ta amince a bata mata suna, da dora mata laifi bisa hujjar yaki da annobar ba.

Yang ya ci gaba da cewa, shekarar bana, kasar Sin za ta yi murnar cika shekaru 100 da kafuwar JKS. Kuma jama’ar Sin sun samu manyan nasarori karkashin shugabanci na gari na JKS, za su kuma kara hada kansu, da kara yin gwagwarmaya, wajen ci gaba da bin hanyar gurguzu mai halin musamman na kasar Sin. Za su kuma kara raya kasar Sin mai wadata, tare da samun farfadowar al’ummar Sinawa.

A nasa bangaren kuwa, Mr. Blinken cewa ya yi, kasarsa na bin manufar “kasar Sin daya tak a duniya”, tare da mutunta yarjejeniyoyin hadin gwiwa guda 3 da Sin da Amurka suka daddale. Bugu da kari, Amurka na fatan rika tuntubar kasar Sin, kan muhimman al’amuran kasa da kasa da na shiyya-shiyya. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan