logo

HAUSA

Amurka Za Ta Dandana Kudarta Sakamakon Yunkurin Hana Ci Gaban Kasar Sin Bisa Sunan Yin Takara

2021-06-09 20:41:59 CRI

Amurka Za Ta Dandana Kudarta Sakamakon Yunkurin Hana Ci Gaban Kasar Sin Bisa Sunan Yin Takara_fororder_中美2

Ranar 8 ga wata, majalisar dattawan kasar Amurka ta zartas da shirin dokar kirkire-kirkire da yin takara, inda aka tanadi wasu shirye-shiryen dokokin hana ci gaban kasar Sin bisa tushen hadin kan jam’iyyu, wadanda suka mayar da kasar Sin tamkar abokiyar gaba ce cikin tunaninsu, sun kuma bata sunan kasar Sin dangane da hanyar raya kasa, da manufofi na cikin gida da na waje, tare da yin shelar yin takara da kasar Sin daga dukkan fannoni bisa manyan tsare-tsare, a yunkurin ingiza rabuwar Sin da Amurka, da yin adawa da juna.

Shirin dokar mai ruhin yakin cacar baka, da tunanin cin moriya ta hanyar faduwar wani, bai dace da ci gaban zamani ba, wanda kuma ya ba mutane mamaki sosai.

Sanin kowa ne cewa, an zartas da shirin dokar ne domin danne kasar Sin daga dukkan fannoni, amma bisa sunan kirkire-kirkire da yin takara. Hakan bai cancanci ainihin ma’anar yin kirkire-kirkire da yin takara ba, haka kuma, wasu Amurkawa sun yi amai sun lashe, dangane da ka’idar yin takara cikin ‘yanci a kasuwa, wacce suka yi ta tsayawa a kai. Wasu kuma sun mayar da shirin dokar a matsayin manufa ta gari, wajen kiyaye danniyar da Amurka ke yi, amma hakika dai za su dandana kudar shirin dokar.

Masu nazarin al’amura sun yi nuni da cewa, abubuwan da aka tanada cikin shirin dokar ba su shafi muhimman batutuwan da ke shafar Amurka ba, don haka shirin dokar ba zai taimaka wajen daidaita matsalolin da Amurka ke fuskanta yanzu ba. A maimakon haka, shirin dokar zai kara gishiri kan zargin wai “Sin na kawo barazana”, inda wasu ‘yan siyasar Amurka suna kara nuna gazawarsu, wajen tafiyar da harkoki da kuma yunkurinsu na dora wa saura laifi.

Yanzu ana raya tattalin arzikin duniya na bai daya. Yadda wasu Amurkawa ke yunkura danne kasar Sin ta hanyar kafa doka zai lahanta ci gaban duniya, a karshe kuma za su dandana kudarsu.

Hakika dai, manufar da kasar Sin ke kokarin cimmawa ba maye gurbin Amurka ba ce. A’a, tana kokarin cimma burinta na ganin al’ummar kasar Sin sun kara jin dadin zamansu ne.

Har kullum kasar Sin na maraba da yin takara cikin adalci, a maimakon yin takarar cin moriya da faduwar wani, tare da yin fada da juna. Haka kuma ba za ta amince a kwace mata ikonta na raya kanta ba. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan