logo

HAUSA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Rika Yi Wa Kamfanoninta Adalci

2021-06-10 19:39:31 CRI

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Rika Yi Wa Kamfanoninta Adalci_fororder_sin

Kakakin ma’aikatar kasuwancin kasar Sin Gao Feng, ya ce kasar sa na fatan kasar Amurka za ta rika yi wa kamfanonin Sin adalci, tare da kauracewa siyasantar da harkokin da suka shafi tattalin arziki da cinikayya.

Gao Feng, wanda ke wannan tsokaci a yau Alhamis, ya jinjinawa aniyar Amurka, na kawar da dokar da tsohon shugaban kasar Donald Trump ya zartas, wadda ta tanaji matsin lamba ga kamfanonin fasahohin sadarwa na Sin da suka hada da TikTok da WeChat. Gao Feng ya ce, matakin gwamnatin Amurka mai ci, ya zo daidai lokacin da ake bukatarsa.

Jami’in ya kara da cewa, dangantakar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka, na haifar da moriyar bai daya tsakanin su.  (Saminu)

Saminu