logo

HAUSA

Bankin duniya: Tattalin arzikin kasar Sin zai bunkasa da kaso 8.5 cikin 100 a bana

2021-06-09 09:36:25 CRI

Bankin duniya: Tattalin arzikin kasar Sin zai bunkasa da kaso 8.5 cikin 100 a bana_fororder_210609-tattalin arzikin Sin

Babban bankin duniya ya bayyana cikin rahotonsa na baya-bayan da ya fitar game da makomar tattalin arzikin duniya cewa, tattalin arzikin kasar Sin zai bunkasa da kaso 8.5 cikin 100 a shekarar 2021, karuwar kaso 0.6 kan hasashen da ya yi a baya.

Darektan rukunin bankin mai kula da hasashen yanayin tattalin arzikin duniya Ayhan Kose, ya shaidawa taron manema labarai cewa, kokarin kasar Sin na dakile annobar COVID-19 cikin sauri, da managartan manufofinta na goyon baya masu muhimmanci, da farfadowar cinikayyar kasa da kasa a baya-bayan, na daga cikin abubuwan da suka taimaka wajen farfadowar kasar Sin matuka.

A cewar wani rahoto da bankin ya saba fitarwa sau biyu a shekara, ana sa ran tattalin arzikin duniya ya bunkasa da kaso 5.6 cikin 100 a shekarar 2021, karuwar kaso 1.5 cikin 100 kan hasashen da aka yi a baya, musamman ganin yadda tattalin arzikin wasu manyan kasashe masu karfin tattalin arziki ya farfado sosai.

Shugaban rukunin babban bankin duniya David Malpass ya bayyana cewa, yayin da ake ganin alamu na farfadowar tattalin arzikin duniya, a hannu guda kuma annobar na ci gaba da haifar ta talauci da rashin daidaito kan jama’a a kasashe masu tasowa dake sassan duniya.

Yana mai cewa, akwai bukatar kasashen duniya su kara kaimi wajen raba alluran rigakafi, da rage basussuka, musamman ga kasashe masu karamin karfi. (Ibrahim)