logo

HAUSA

Sin da Amurka sun amince su hada kai wajen warware wasu muhimman matsaloli a fannin tattalin arziki da cinikayya

2021-06-03 20:46:32 CRI

Sin da Amurka sun amince su hada kai wajen warware wasu muhimman matsaloli a fannin tattalin arziki da cinikayya_fororder_微信图片_20210603205116

Ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin ta fada Alhamis din nan cewa, kasashen Sin da Amurka, sun fara tuntubar juna a fannonin tattalin arziki da cinikayya, inda suka amince su hada kai, don ganin sun warware wasu muhimman matsaloli a zahiri.

Da yake karin haske game da tattaunawar kafar bidiyo ta baya-bayan da jami’an kasashen biyu suka yi, mai magana da yawun ma’aikatar ciniyayya ta kasar Sin Gao Feng, ya bayyana tattaunawar tsakanin sassan biyu a matsayin mai armashi.

Mataimakin firaministan kasar Sin Liu He, mamba a hukumar siyasa ta kwamitin koli na JKS, kana jagoran bangaren Sin a tattaunawar tattalin arziki tsakanin Sin da Amurka, ya tattauna ta kafar bidiyo da wakiliyar cinikayya ta Amurka Katherine Tai a ranar 27 ga watan Mayu, da kuma sakatariyar bailtun malin Amurka Janet Yellen a jiya 2 ga watan Yuni.