logo

HAUSA

Farfadowar Cinikayyar Wajen Kasar Sin Ta Samar Da Tabbaci Ga Farfadowar Tattalin Arzikin Duniya

2021-06-07 21:13:53 CRI

Farfadowar Cinikayyar Wajen Kasar Sin Ta Samar Da Tabbaci Ga Farfadowar Tattalin Arzikin Duniya_fororder_sin

Sabbin alkaluman da babbar hukumar kwastan ta kasar Sin ta fitar a ranar 7 ga watan nan, dangane da harkokin shige da fice sun nuna cewa, a watanni 5 na farkon shekarar bana, jimilar darajar kayayyakin shige da fice na kasar Sin ta karu da kaso 28.2 bisa dari idan an kwatanta da na makamancin lokaci na shekarar bara, ciki kuma darajar kayayyakin da ake shigarwa kasar darajar su ta karu da kaso 30.1, yayin da darajar kayayyakin da ake fitarwa ta karu da kaso 25.9. Ya zuwa watan Mayun bana kuma, watanni guda 12 ke nan a jere, kayayyakin shige da fice sun karu a kasar Sin.

Ga alama kasar Sin ta samu farfadowar cinikin waje ba tare da wata matsala ba, lamarin da ya goyi baya da karfafa gwiwar kasashen duniya ta fuskar farfado da tattalin arziki. Ina dalilin da ya sa haka? Saboda kasar Sin ta samu nasarar dakile da kandagarkin cutar COVID-19, ta ba da jagora wajen komawa bakin aiki, da dawo da harkokin kasuwanci, da na samar da kayayyaki. Sa’an nan gwamnatin kasar Sin, sana’o’i daban daban na kasar da ma kamfanonin kasar sun yi kokari tare.

Musamman ma gwamnatin Sin ta fitar da wasu manufofi kan lokaci, a kokarin goyon bayan kamfanonin Sin da ke gudanar da cinikin waje yadda ya kamata.

Muna iya kara sanin hakan, bisa takardun neman sayen kaya da kamfanonin Sin da ke gudanar da cinikin waje suka samu. Wani kamfanin da ke birnin Ningbo na lardin Zhejiang, wanda ke sayar da na’urar tura kwale-kwale masu amfani da wutar lantarki da makulli, ya yi nuni da cewa, takardun neman sayen kayayyakinsa ya karu fiye da kaso 60 a bana, kana ya tsara ajandar aikinsa har zuwa watan Maris mai zuwa. Kamfanonin kasar Sin da ke gudanar da cinikin waje kamar shi suna da yawa.

Takardar tambaya da ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ta yi wa kamfanoni fiye da dubu 20 da suka halarci taron baje kolin harkokin ciniki a birnin Guangzhou karo na 129 a kwanan baya ya shaida cewa, kamfanonin da yawansu ya kai kaso 43.2 ne za su dauki watanni 3 ko fiye da haka, suna kera kayayyaki bisa takardun neman sayen kayayyakinsu.

Dangane da kayayyakin da kasar Sin take shigowa da su kuwa, sakamakon farfadowar masana’antu da yin sayayya a kasar Sin, ya sa bukatun kasar Sin kan kayayyakin kasa da kasa suke karuwa. A watanni 5 na farkon bana, yawan rairayin karfe, danyen mai, wake da kasar Sin take sayowa daga ketare, da kuma farashinsu dukkansu suna karuwa.

Kana kuma, karuwar yawan injuna da kayayyakin lantarki da kasar Sin take sayowa daga ketare ta kai kaso 21.8, ciki kuma akwai motoci dubu 429, wadanda yawansu ya karu da kaso 54.2. Ma iya cewa, farfadowar kasuwar kasar Sin tana kara kuzari, ga farfadowar tattalin arziki da cinikin duniya.

Kowa na iya ganin cewa, ba za a iya maye muhimmin gurbin kasar Sin cikin tsarin masana’antun kasa da kasa, da kuma tsarin samar da kayayyaki na kasa da kasa ba. Kasuwar kasar Sin mai karfin gaske ta samar wa kamfanonin ketare na kasa da kasa babbar riba, wadda ba za su iya kau da ido daga gare ta ba. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan