logo

HAUSA

Tattalin arzikin kasar Sin ya farfado, harkokin kasuwanci kuma sun koma yadda suke

2021-06-08 11:27:18 CMG

Tattalin arzikin kasar Sin ya farfado, harkokin kasuwanci kuma sun koma yadda suke_fororder_tattali

Shugaban ofishin binciken harkokin kudi na kasar Sin, Hou Kai, ya ce tattalin arzikin kasar ya farfado kuma harkokin kasuwanci sun koma yadda suke sannu a hankali a shekarar 2020, duk da annobar COVID-19 da ta barke.

Bisa umarnin majalisar gudanarwar kasar Sin, Hou Kai ya mika rahoton bincike game da yadda aka aiwatar da kasafin kudin gwamnatin tsakiya na shekarar 2020 da sauran kudaden shiga da wadanda aka kashe, yayin zaman zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin dake gudana.

A cewarsa, Kasar Sin ta rage matsin dake kan harkokin kasuwanci da sama da yuan triliyan 2.6, kwatankwacin dala biliyan 406.48 a 2020. Ya kara da cewa, an kuma samar da sabbin guraben ayyukan yi miliyan 11.86 a birane kana karin mutane miliyan 9.6 ne suka kaura daga wuraren da ba su dace da rayuwa ba. (Fa’iza Mustapha)

Bello