logo

HAUSA

Babban taron WHO ya sake watsi da shawarar dake shafar Taiwan bisa ka’idar Sin daya kacal a duniya

2021-05-25 20:46:20 CRI

Babban taron WHO ya sake watsi da shawarar dake shafar Taiwan bisa ka’idar Sin daya kacal a duniya_fororder_1

A jiya Litinin ne hukumar gudanarwar babban taron hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO, a karo na 74 ta zartas da kudurin cewa, ba za ta yarda da shawarar da wasu kasashe suka gabatar ba, game da gayyatar jihar Taiwan ta kasar Sin ta halartar babban taron WHO bisa matsayinta na ‘yar kallo. Lamarin da ya sake nuna cewa, ba zai yiwu a haifar da barazara ga ka’idar kasar Sin daya kacal a duniya ba. Kuma ko shakka babu ba za a cimma dukkanin yunkurin hakan ba.

Ya zama wajibi a daidaita batu game da halartar yankin Taiwan babban taron WHO, bisa ka’idar kasar Sin daya kacal a duniya, saboda tuni aka zartas da kudurin da ya shafi hakan, karkashin kudurorin babban taron MDD mai lambar 2758, da na babban taron WHO mai lambar 25.1.

Hakika al’ummun kasa da kasa sun fahimci lamarin sosai, kafin kaddamar da babban taron WHO karo na 74, sai da kasashe sama da 150 suka fitar da sanarwar diplomasiyya, domin nuna goyon bayan kudurin kasar Sin na rashin amincewa da halartar yankin Taiwan babban taron WHO na bana, kuma kasashen duniya sama da 80 sun rubuta sakwanni zuwa ga hukumar kiwon lafiya ta duniya, inda suka bayyana cewa, suna nacewa kan ka’idar kasar Sin daya kacal a duniya, kuma ba za su yarda da yankin Taiwan ya halarci babban taron hukumar ba. A bayyane take cewa, kusan daukacin kasashen duniya suna amincewa da ka’idar kasar Sin daya kacal a duniya.

Ya dace a fahimci cewa, babban taron WHO ba wurin neman samun moriyar siyasa ba ne, duk da cewa wasu kasashen yamma suna siyasantar da batun kiwon lafiya, yunkurinsu zai iya kawo illa ga gudanar babban taron, har ma ya yi mummunan tasiri ga hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa, wajen kandagarkin annobar cutar COVID-19. (Jamila)