logo

HAUSA

Yadda Amurka Take Goyon Bayan Shigar Yankin Taiwan Babban Taron WHO Ya Siyasantar Da Batun Kiwon Lafiya

2021-06-02 15:39:17 CRI

Yadda Amurka Take Goyon Bayan Shigar Yankin Taiwan Babban Taron WHO Ya Siyasantar Da Batun Kiwon Lafiya

Daga Amina Xu

Kwanan baya, jakadiyar Amurka dake Najeriya Mary Beth Leonard, ta wallafa bayani mai taken “Hana Taiwan shiga taron WHO, ya lahanta kokarin da ake yi na inganta kiwon lafiyar duniya” a jaridar 《Vangard》, inda ta ce Sin ta yi kuskure wajen hana yankin Taiwan shiga babban taron WHO. To amma mene ne gaskiyar abin da ya faru?

A ran 24 ga watan Mayun da ya wuce, kwamitin gudanarwa na babban taron WHO karo na 74, da kuma daukacin mambobinsa, sun ki yarda da shirin da wasu kasashe suka gabatar, na wai a gayyaci yankin Taiwan, don shiga babban taron WHO a matsayin mai sa ido.

Abun tambaya a nan shi ne, shin Sin ita kadai ce ta yanke wannan shawara? Amsa ita ce A’a. A hakika mambobin kasashe 150, ciki hadda Najeriya daga cikin jimillar kasashe 194 na hukumar WHO, sun amince su goyi bayan kasar Sin kan wannan lamari. Ban da wannan kuma, sauran kasashe fiye da 80, sun mikawa WHO wasika, don bayyana niyyarsu ta nacewa ga ka’idar “Kasar Sin daya tak a duniya”, don bayyana kin yarda da shigar yankin Taiwan cikin wannan taro. Shin wadannan kasashe dukkansu sun yi kuskure ke nan?

Hukumar kiwon lafiya WHO, wata hukuma ce dake karkashin MDD, ita ce kuma hukumar kiwon lafiya mafi girma a duniya. Kuma kasashe dake da ikon mulki kai ne kadai ke iya shiga hukumar. Amma Taiwan wani yanki ne cikin kasar Sin.

Baya ga haka, kuduri mai lamba 2758 na babban taron MDD da aka zartas a watan Oktomban shekarar 1971, da kuma kuduri mai lamba 25.1 na babban taron WHO da aka zartas a watan Mayu na shekarar 1972, sun amince da ka’idar “kasar Sin daya tak a duniya”. Don haka kamata ya yi kasashen duniya ciki hadda Amurka su yi biyayya ga wannan ka’ida.

Mary Beth Leonard ta bayyana a cikin bayaninta cewa, wai hana Taiwan shiga babban taron, zai lahanta kokarin da duniya ke yi, wajen yakar cutar COVID-19, har ma hakan zai kawo cikas ga aikin kiwon lafiya na Najeriya. A hakika hakan abun dariya ne kawai.

Da farko, gwamnatin kasar Sin, ta baiwa yankin damar shiga harkokin kiwon lafiyar duniya bisa ka’idar “Sin daya tak a duniya”. Tun barkewar cutar, gwamnatin ta gabatarwa yankin bayanai har 260 kan cutar. Ban da wannan kuma, masanan yankin sun shiga ayyukan WHO sau 16. Kaza lika sakatariyar WHO ta kan sanar da yankin bayanan cutar ko da yaushe.

Zancen da ta yi, cewa wai akwai gibin kandagarkin cutar tsakanin babban yankin kasar Sin da yankin Taiwan ba gaskiya ba ne. Mun san kwararrun Taiwan ba su rasa samun hanyoyi da dandaloli na yin musayar dabaru da fasahohin kandagarki da sauran sassan duniya, irin wadanda ba za su lahanta kokarin da duniya ke yi na dakile cutar cikin hadin kai ba.

Na biyu, cutar tana kan ganiyarta a yankin Taiwan, yayin da yawan mutanen da ake tabbatarwa na kamuwa da cutar a ko wace rana ke kusan haura dubu 1. Bisa wadannan alkaluma, yankin ba shi da cikakken karfin tinkarar matsalar da kan sa, balle ya taimakawa sauran kasashe ciki hadda Najeriya idan ma ya halarci taron?

Na uku, Sin tana kokarin taimakawa sauran kasashe wajen dakile cutar, musamman ma yadda take tallafawa kasashe masu tasowa ciki hadda Najeriya. A gun babban taro WHO da aka yi a wannan karo, kasashe da dama na nuna godiya matuka, ga taimakon da Sin take ba su, a fannin samar da alluran rigakafi a kyauta, da tura masanan kiwo lafiya zuwa kasashe daban-daban, da samar da kimiyya da dai sauransu.

Ban da wannan kuma, Sin ta bayyana sau da dama, niyyarta ta taimakawa yankin Taiwan wajen dakile cutar. Amma jami’an yaki da cututuka na yankin, sun ki yarda da karbar kayayyakin tallafi daga babban yankin Sin, bisa hujjoji daban-daban. Abun da ya kawo cikas matuka ga yankin, wajen samar da isassun alluran.

Shin ko mece ce matsayar Amurka kan wannan batu? Jakadan yankin na Taiwan a Amurka Hsiao Bi-Khim, ta bayyana imaninta sosai, game da kokarin tuntubar Amurka, bisa alkawarin da shugaba Joe Biden ya yi a kwanan baya na samarwa kasashen duniya allurai miliyan 20. Amma a hakika magajin birnin Taipei Ko Wen-je ya ce, har zuwa yanzu Amurka ba ta samar wa yankin allura ko daya ba.

Sin tana son taimakawa yankin Taiwan bisa zuciya daya, amma wasu ‘yan siyasar yanki suna kin yarda. Yayin da wasu kasashe kuma ke yin biris da kokarin da kasar Sin ke yi, wajen taimakawa sauran kasashe a yakin da suke yi da cutar. A maimakon haka, Amurka tana taimakawa sauran kasashe da fatar baki kawai.

Cutar COVID-19 abokiyar gabar dukkanin Bil Adama ce, don haka kamata ya yi kasa da kasa su kara hadin kansu don yakar cutar tare. Kuma ya kamata ‘yan siyasar wasu kasashe su daina yunkurinsu na ci gaba da dora laifi kan wasu, da siyasantar da batun kiwon lafiya, da ma tsoma baki cikin harkokin gidan sauran kasashe. (Amina Xu)