logo

HAUSA

Shugaban kasar Namibia da mai dakinsa sun kamu da COVID-19

2021-05-28 16:00:49 CRI

Shugaban kasar Namibia, Hage Geingob, da uwar gidansa Monica Geingos, sun kamu da cutar COVID-19, sakamakon gwajin da aka yi musu a ranar Laraba ya nuna sun kamu da cutar.

Sai dai shugaban da mai dakin nasa suna cikin yanayi mai kyau kuma sun riga sun killace kansu a cikin gidansu, sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar a yammacin ranar Alhamis ta yi musu fatan samun warka cikin hanzari.(Ahmad)

Ahmad