logo

HAUSA

Ya Dace Amurka Da Kawayenta Su Ba Da Damar Gudanar Da Binciken Gano Asalin COVID-19 A Kasashensu

2021-06-02 18:35:00 CRI

Ya Dace Amurka Da Kawayenta Su Ba Da Damar Gudanar Da Binciken Gano Asalin COVID-19 A Kasashensu_fororder_amurka

A yayin da wasu sassan duniya ke ci gaba da fama da annobar COVID-19, har yanzu wasu ’yan siyasar Amurka ba su sauya halayensu na neman shafawa kasar Sin bakin fenti ba, ta hayar fakewa da batun binciken gano asalin cutar COVID-19.

Sanin kowa ne cewa, a baya wata tawagar kasa da kasa da WHO gami da takwarorinsu dake kasar Sin, sun gudanar da aikin binciken gano asalin kwayar cutar COVID-19 a birnin Wuhan ba tare da wata rufa-rufa, daga karshe kuma aka fitar da sakamakon binciken da kusan daukacin duniya ta yi na’am da shi.

Amma abin mamaki shi ne, Amurka tana nuna shakku kan wannan batu, har shugaba Joe Biden ya umarci hukumar leken asirin kasar, wai ta gudanar da wani bincike kan rahoton cikin kwanaki 90 ta kuma fito da sakamako. Idan har Amurka tana nuna shakku kan binciken da aka yi, to ya kamata ta ba da dama a gudanar da irin wannan bincike a kasarta ba tare da nuna son kai ba.

A baya, Amurka tana tunanin wai, cutar ta bullo ne daga dakin bincike, idan har ta karyata sakamakon binciken masana, to ya dace ta fara budewa duniya, dakin gwajin kwayoyin halitta na Fort Detrick da aka yi masa lakabi da “sansanin gwajin sinadarai da tunanin Bil Adama na hukumar leken asiri ta Amurka” domin a gudanar da irin wannan cikakken bincike a kansa.

Bayanai na nuna cewa, an rufe wannan daki a watan Yuli na shekarar 2019, amma tun ba a je ko’ina ba, wata cuta mai nasaba da tabar lantarki ta barke a wata unguwa dake kusa da wannan daki a jihar Virginia, wadda ta yi kama da cutar COVID-19. Shin me ya sa Amurka ta rufe wannan daki a wancan lokaci? Ko yana da alaka da cutar, ko Amurka ta boye wani abu a cikin wannan daki? Don haka, bincike ne kadai zai amsa wadannan tambayoyi da duniya ke bukatar amsoshin su.

Baya ga wannan dakin bincike, Amurka ta boye irin wadannan dakunan gwajin halittu fiye da 200 dake sassa daban-daban na duniya, ba tare yiwa duniya wani bayani game da abubuwan da ake yi a cikinsu ba.

Koma dai mene ne, yanzu haka dai an kammala aikin binciken gano asalin wannan cuta a kasar Sin, har an fitar da cikakken sakamako. Yanzu ya dace Amurka da sauran kasashe, su ma su ba da irin wannan hadin kai, wajen ganin an gudanar da cikakken aikin binciken gano asalin wannan cuta a kasashensu daga dukkan fannoni, ba kuma tare da wata rufa-rufa ba.

Aikin binciken gano asalin kwayar cutar numfashi ta COVID-19, aiki ne na masana kimiyya, ba na masu leken sirri ko neman bata sunan sauran kasashe don biyan wata bukata ta siyasa ba. Gwano aka ce, ba ya jin warin jikinsa. (Ibrahim Yaya)

Ibrahim Yaya