logo

HAUSA

Manyan kungiyoyin duniya hudu sun yi kira ga kasa da kasa da su zuba kudi dala biliyan 50 don gaggauta kawo karshen cutar COVID-19

2021-06-02 14:31:44 CRI

Manyan kungiyoyin duniya hudu sun yi kira ga kasa da kasa da su zuba kudi dala biliyan 50 don gaggauta kawo karshen cutar COVID-19_fororder_54674e7b1f6f4818a8a9d7d195c29c59

Babban daraktan kungiyar kiwon lafiyar duniya ta WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, da daraktar kungiyar cinikayya ta duniya WTO Ngozi Okonjo-Iweala, da shugabar asusun ba da lamuni na duniya na IMF Kristalina Georgieva, da ma shugaban bankin duniya David Malpass, sun wallafa wani bayanin hadin gwiwa, a wasu jaridun kasashe daban daban, a jiya 1 ga watan Yuni.

Cikin jawabin na su, sun nuna cewa, akwai babban gibi a tsakanin kasasahe masu sukuni da marasa ci gaba, a fannin samun allurar rigakafin cutar COVID-19, lamarin da ya haddasa bullar sabbin nau’o’in kwayoyin cutar, wadanda ke haifar da sake barkewar annobar a kasashe masu tasowa.

Haka kuma bayanin ya nuna cewa, samun allurar rigakafin cuta na da matukar muhimmanci, wajen ganin bayan ta, da ma sa kaimi ga farfadowar duniya baki daya. Akwai kuma yiwuwar kawo karshen cutar, sai dai ana bukatar duk duniya ta dauki mataki ba tare da bata lokaci ba.

A cikin bayanin, shugabannin hudu sun yi kira ga kasashe daban daban, da su zuba kudi har dala biliyan 50, domin goyon bayan wani tsarin samun allurar rigakafin cutar COVID-19 na duniya, a kokarin gaggauta kawo karshen cutar COVID-19, da ma tabbatar da farfadowar dukkanin duniya.

Ban da wannan kuma, shugabannin hudu sun kira wani taron manema labarai a ranar, inda shugabar IMF Kristalina Georgieva ta furta cewa,

“Kila za ku tambaya, me ya sa IMF ta mai da hankali kan batun samun allurar rigakafin? Dalilin da ya sa haka shi ne, bambancin matsalar yaki da cutar COVID-19 a tsakanin kasashe mawadata da matalauta, na haddasa babban bambancin farfadowar tattalin arziki a tsakaninsu, lamarin da ya kawo illa sosai ga dukkan kasashe. Alkaluma na nuna cewa, yiwa al’ummun duniya allurar hanya ce mafi kyau ta kyautata aikin samarwa dukkanin duniya rigakafin cikin kankanin lokaci. Ma iya cewa, manufar allurar rigakafin, manufa ce da ta shafi tattalin arziki.”

Ana sa ran cewa, wannan shirin da za a kashewa dala biliyan 50, zai samar da ribar tattalin arziki ta dala triliyan 9 nan zuwa shekarar 2025. A ciki kaso 60 bisa dari zai amfani kasashe masu tasowa, yayin da kaso 40 zai amfani kasashe masu ci gaba.

A yayin taron manema labaran, babban daraktan kungiyar WHO Tedros Ghebreyesus, ya mara baya ga shirin. Yana mai cewa,

“Abin da muke farin cikin gani shi ne, a cikin shirin, a samu yawancin sabbin kudade ta hanyar ba da tallafi kyauta cikin sauri. A kokarin rage gibin kudade na shirin samar da matakan gaggauta yaki da COVID-19. Lamarin da zai taimaka mana wajen kara yawan na’urorin jinya, da ma hakaba aikin samar da allurar rigakafin. A kokarin rarraba su cikin adalci.”

A nasa bangaren, shugaban bankin duniya David Malpass ya yi tsokaci da cewa, ya kamata kasashe masu sukuni su gaggauta samar da allurar rigakafin ga sauran kasashe, ya kara da cewa,

“Matakin gaggawa shi ne, wadancan kasashen da ke da isassun allurar rigakafin, su gaggauta samar da su ga kasashen da ke da shirin yin rigakafin. Bankin duniya na samun hada-hadar kudi ta alluran, da adadin dala biliyan 12. Idan akwai bukata, muna iya samar da karin kudi, domin taimakawa kasashe daban daban, wajen saye da rarraba allurar, da ma karfafa gwiwar yin alluran. Ya zuwa karshen watan Yuni, za mu kara azama ga kasashe fiye da 50 wajen yin alluran.”

Haka zakila, babbar daraktar kungiyar WTO Ngozi Okonjo-Iweala ta ce, cinikayya za ta sa kaimi ga karuwar yawan allurar rigakafin da za a samar. Ta furta cewa,

“Manufar allurar rigakafin, manufa ce da ta shafi cinikayya. Idan ba a dauki matakai a fannin cinikayya ba, ba za mu samun karuwar yawan allurar da za a samar ba. Haka kuma idan ba mu iya warware matsalar karancin alluran ba, to ba za a iya samun dauwamammen ci gaban cinikayya da farfadowar tattalin arziki ba. Muna fatan ceton rayuka ta hanyar hadin kan kasa da kasa.”(Kande Gao)