logo

HAUSA

Jami’in MDD ya bukaci a hada kai da Afrika don yakar annobar COVID-19

2021-05-26 13:01:48 CRI

Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya bukaci manyan kasashen duniya da su hada kai da kasashen Afrika don yaki da cutar COVID-19.

A jawabinsa na ranar Afrika, wanda ta fado a ranar 25 ga watan Mayu, Guterres ya ce, bayan kawo karshen annobar, akwai bukatar taimakon juna wajen farfadowar tattalin arziki da cimma nasarar shirin samar da dauwamaman cigaba, akwai bukatar a tabbatar da yin raba daidai ga tsarin rarraba alluran riga-kafin cutar COVID-19.

A cewarsa, a halin yanzu, akwai babban gibi a tsarin rarraba alluran riga-kafin a tsakanin kasashen duniya. Alkaluman baya bayan nan sun nuna cewa, har ya zuwa yanzu, kasashen Afrika sun samu kaso biyu bisa 100 ne kawai na riga-kafin. Ya ce a wannan rana ta Afrika, yana jaddada yin kira ga manyan kasashen duniya da su hada kai da Afrika.

Ya ce annobar COVID-19 ta jefa duniya cikin yanayin karayar tattalin arziki, lamarin da ya kara bayyanawa a fili girma banbancin dake tsakanin kasashe masu sukuni da marasa galihu. Lamarin yana haifar da koma bayan cigaba a dukkan kasashen Afrika.

Mista Guterres ya ce, annobar ta kuma bayyana abubuwan dake janyo tashe tashen hankula ta hanyar kara girma rashin daidaito da kuma bayyana girma gazawar shugabanci na gwamnatocin wasu kasashen duniya da dama, musamman wajen tafiyar da fannonin muhimman ababen more rayuwa kamar kiwon lafiya, ilmi, lantarki, samar da ruwa da tsaftar muhalli.(Ahmad)