logo

HAUSA

Shugaba Xi ya aike da sakon taya murnar bude baje kolin China-CEEC karo na biyu

2021-06-08 19:28:42 CRI

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon taya murnar bude baje koli karo na biyu, na hadin gwiwar Sin da kasashen tsakiya da gabashin nahiyar Turai ko China-CEEC.

Cikin sakon da ya aike a Talatar nan, shugaba Xi ya yi fatan ganin dukkanin sassan dake da ruwa da tsaki a shirya baje kolin, sun yi amfani da damar dake cikin sa, wajen cin gajiyar hadin gwiwa da fadada cudanya.

An bude baje kolin na China-CEEC ne a birnin Ningbo dake lardin Zhejiang na gabashin kasar Sin.  (Saminu)

Saminu