logo

HAUSA

Xi Jinping: Karfafawa da inganta yin mu’amala da cudanyar bayanai a tsakanin Sin da kasashen ketare don nuna ainihin Sin

2021-06-01 15:50:37 CRI

Da yammacin jiya Litinin 31 ga watan Mayu ne, ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya gudanar da zaman nazari karo na 30, game da karfafa dabarun yin mu’amala da cudanyar bayanai a tsakanin Sin da kasashen ketare.

Yayin da yake jagorantar zaman, shugaban kasar, kuma babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya jaddada cewa, wajibi ne Sinawa su yayata labarin kasar su, su watsa muryar Sinawa, tare da bayyana gaskiya.

Shugaba Xi ya ce, nuna wa kasashen duniya ainihin kasar Sin daga dukkan fannoni ba tare da boye kome ba, na da matukar muhimmanci a fannin karfafa ayyukan yin mu’amala da cudanyar bayanai a tsakanin Sin da kasashen ketare. Wajibi ne a kara sanin muhimmanci da wajibcin inganta da kyautata ayyukan yin mu’amala da cudanyar bayanai a tsakanin Sin da kasashen ketare a sabon halin da ake ciki. Kaza lika wajibi ne a yi aiki tukuru, wajen karfafa yin mu’amala da cudanyar bayanai a tsakanin Sin da kasashen ketare. Hakan kuma zai samar da damar hade burin wanzuwar cikakken karfin kasar Sin, da matsayin ta a idanun duniya, baya ga gudummawar da hakan zai bayar, wajen gina al’umma daya mai kyakkyawar makoma ga dukkanin bil Adama.  (Saminu)

Saminu