logo

HAUSA

Shugaban kasar Sin ya jaddada bukatar karfafa kimiyya da fasaha a muhimman matakai

2021-05-29 15:47:12 CMG

Shugaban kasar Sin ya jaddada bukatar karfafa kimiyya da fasaha a muhimman matakai_fororder_kimiiya

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira da a kara kokarin karfafa kasar, ta yadda za ta zamo jagora a fannin kimiyya da fasaha, kuma mai karfi da dogaro da kanta a wannan fanni.

Xi Jinping ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi ga taron mambobin kwalejin kimiyya da aikin Injiniya ta kasar Sin CAE da na kungiyar masana kimiyya da fasaha ta kasar CAST.

A cewarsa, ya kamata a rika daukar batun dogaro da kai da samun karfi a fannin kimiyya da fasaha a matsayin hanyar tallafawa ci gaban kasar.

Ya kara da cewa, wajibi ne aikin raya kimiyya da fasaha na kasar ya kasance kan gaba a duniya, kana ya taka rawa a fannin tattalin arziki da kokarin cimma bukatun kasar tare da amfanawa al’ummarta. (Fa’iza Mustapha)

Faeza