logo

HAUSA

Shugaba Xi Ya Fara Rangadi A Lardin Qinghai

2021-06-07 21:10:57 CRI

Shugaba Xi Ya Fara Rangadi A Lardin Qinghai_fororder_xi

A yau Litinin ne shugaban kasar Sin, kuma babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya fara rangadi a lardin Qinghai dake arewa maso yammacin kasar Sin.

Da yammacin yau din, Xi ya ziyarci kamfanin samar da kafet na Shengyuan na Qinghai dake birnin Xining, don ganewa idanun sa yadda kamfanoni ke dogaro da albarkatun kayayyakin sarrafawa dake yankunan su, da dabarun kyautata hajoji, da na inganta damar takarar hajojin a kasuwani, da yadda suke ingiza damar samar da guraben ayyukan yi, da samar da karin kudaden shiga ga al’ummun su.

Daga bisani kuma, Xi Jinping ya ziyarci unguwar al’ummar Wentingxiang, don ganin yadda suke aikin raya jami’yya tun daga matakin farko, da inganta ayyukan gudanarwa, da bunkasa hadin kan sassan al’ummu daban daban, da kuma samar da ci gaba.  (Saminu)

Saminu