logo

HAUSA

Shugaba Xi Ya Ziyarci Gundumar Gangcha Dake Lardin Qinghai

2021-06-08 22:02:23 CRI

Shugaba Xi Ya Ziyarci Gundumar Gangcha Dake Lardin Qinghai_fororder_1127543877_16231577222881n

Shugaba Xi Ya Ziyarci Gundumar Gangcha Dake Lardin Qinghai_fororder_xi

Shugaba Xi Ya Ziyarci Gundumar Gangcha Dake Lardin Qinghai_fororder_1127543877_16231577355381n

Shugaban kasar Sin kuma babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya ziyarci gundumar Gangcha dake yankin Haibei na kabilar Tibet mai cin gashin kai, yayin da yake ci gaba da rangadi a lardin Qinghai dake arewa maso yammacin kasar Sin.

A tafkin Qinghai, shugaba Xi ya saurari matakan da ake aiwatarwa na kare muhallin halittu, da sauran sassan muhalli a tsaunukan Qilian da tafkin Qinghai. Kaza lika ya ganewa idanun sa irin ci gaban da aka samu, wajen kyautata kula da muhalli, da yadda ake kare sassan rayuwa a tafkin Qinghai.

Daga baya kuma, Xi Jinping ya ziyarci al’ummar Tibet dake kauyen Guoluozanggongma, na garin Shaliuhe, ya kuma ziyarci gidajen su domin fahimtar yanayin ayyukan su da kuma yanayin rayuwar su.   (Saminu)

Saminu