logo

HAUSA

Shugaba Xi ya taya Herzog murnar lashe zaben shugabancin Isra’ila

2021-06-08 19:33:18 CRI

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya taya Isaac Herzog murnar lashe zaben shugabancin Isra’ila. Cikin sakon da ya aike ga sabon shugaban na Isra’ila a Talatar nan, shugaba Xi ya bayyana cewa, a shekarun baya bayan nan, Sin da Isra’ila na kara daga matsayin musayarsu a dukkanin fannoni, yayin da hadin gwiwar su ke ci gaba da fadada.

Xi ya ce, kasar sa na kara dora muhimmancin gaske, ga bunkasa alakar Sin da Isra’ila, kuma za ta yi aiki tare da Mr. Herzog, wajen karfafa amincewa da juna a fannin siyasa tsakanin su, da zurfafa hadin gwiwar cin moriyar juna a sassa daban daban, da ma daga matsayin cikakken yanayin hadin kai a fannin kirkire kirkire, tsakanin sassan biyu zuwa wani sabon mataki, ta yadda hakan zai amfani kasashen biyu da ma al’ummun su.(Saminu)

Saminu