logo

HAUSA

Sabbin Matakan Kasar Sin Za Su Kara Azama Kan Hadin Gwiwar Kasa Da Kasa Wajen Yaki Da Annobar COVID-19

2021-05-22 16:43:13 CRI

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron kolin lafiya na kasa da kasa, tare da gabatar da jawabi ta kafar bidiyo daga nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin a jiya da dare.

A jawabin nasa, shugaba Xi ya yi kira ga kasashe mambobin kungiyar G20 da su sauke nauyi dake wuyansu wajen hada kan kasa da kasa ta fuskar yaki da annobar COVID-19, ya kuma bayyana ra’ayinsa a fannoni guda 5 tare da sanar da sabbin matakai 5. A daidai wannan muhimmin lokacin da ake ciki na yaki da annobar a duniya, bayanan da kasar Sin ta yi sun nuna wa kasashen duniya manufar hada kai wajen yaki da annobar, tare da kara kuzari a fannin. An tanadi ra’ayin kasar Sin a wasu fannoni cikin sanarwar taron kolin, lamarin da ya shaida cewa, kasashen duniya sun amince da kyawawan fasahohin kasar Sin da kuma hazakar al’ummar Sinawa.

Kasar Sin ta bayyana ra’ayinta kan goyon bayan yaki da annobar a duniya, tare da daukar hakikanin matakai. Alal misali, kasar Sin ta bai wa kasashe masu tasowa fiye da 80 masu matukar bukata, gudummowar rigakafi. Ta kuma sayar wa kasashe 43 rigakafin. Yawan rigakafin da kasar Sin ta samar a duniya ya kai miliyan 300 baki daya, wadanda kasashe masu tasowa ne suka yi amfani da su wajen yaki da annobar, lamarin da ya kara rahusar riga kafin da azama kan amfani da shi tsakanin al’umma masu yawa. Yayin da ake daidaita rashin tabbas kan yaduwar annobar a duniya, sabbin matakai guda 5 da shugaba Xi ya sanar a yayin taron kolin sun kara kuzari kan hadin gwiwar kasa da kasa wajen yaki da annobar a kan lokaci.

Kasar Sin za ta kara samar da taimakon kudi na dalar Amurka biliyan 3 cikin shekaru 3 masu zuwa, a kokarin taimakawa kasashe masu tasowa wajen yaki da annobar da farfado da tattalin arziki da zaman al’ummar kasa. Haka kuma kasar Sin za ta kara samar wa duniya rigakafin. Kana tana goyon bayan more fasahar rigakafin da kasashen duniya, da hadin gwiwa ta fuskar samar da rigakafin da kawar da sharadin ‘yancin mallakar fasahar riga kafin COVID-19. Har ila yau kasar Sin ta yi kira da a kafa dandalin tattaunawar duniya kan hadin gwiwa dangane da rigakafin, a kokarin kara azama kan rarraba rigakafin a duniya cikin adalci. Wadannan matakai sun sassauta damuwar da kasashen duniya suke nunawa a yanzu, sun kuma taimaka wajen kyautata karfin kasashe masu tasowa na yaki da annobar da kuma karfin zuciyarsu. Kamar yadda wani masanin ilmin huldar da ke tsakanin kasa da kasa na kasar Kenya ya fada, yadda kasar Sin take samar wa kasashen Afirka da dama rigakafin, ya nuna yadda kasar ta sauke nauyi dake wuyanta, ta kuma nuna aniyarta wajen daidaita matsala tare da kasashen Afirka. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan