logo

HAUSA

Wajibi ne a rika wanke hannun jarirai a hankali don kare su daga annobar COVID-19

2021-06-07 17:19:15 CRI

Wajibi ne a rika wanke hannun jarirai a hankali don kare su daga annobar COVID-19_fororder_u=1734653084,1554662158&fm=193&f=GIF

Yayin da muke dakile da kuma kandagarkin annobar cutar numfashi ta COVID-19, wajibi ne mu mai da hankali kan jarirai ‘yan kasa da shekara guda a duniya, saboda kanana ne sosai, su kan samu matsalar numfashin cikin sauki sakamakon sanya marufin baki da hanci. To yaya za a kare su daga annobar? Madam Zhang Chuji, wata likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi mana karin bayani da cewa, ana kare jarirai ‘yan kasa da shekara guda a duniya daga annoba ta hanyar kare iyayensu yadda ya kamata. Abin da ya kamata a lura da shi, shi ne a rika wanke hannun jariran a tsanake, duk da cewa a kan shafa musu sabulu a hannunsu ko sinadarin kashe kwayoyin cuta, yayin da ake waje.

Madam Zhang ta kara da cewa, kafin iyaye su fara wasa ko rungumar jariransu, dole ne su wanke hannunsu a tsanake da ruwan da ke gudana tare da sabulu ko sinadarin wanke hannu har fiye da tsawon dakikoki 20. Yayin da suke wasa a waje, wajibi ne iyaye su tsabtace hannunsu da sinadarin wanke hannu. Amma duk da haka, bayan da suka koma gida, ya zama tilas iyaye su sake hannunsu a tsanake da ruwan da ke gudana tare da sabulu.

Idan iyayen sun kamu da ciwo, musamman ma idan sun fara yin zazzabi, ko tari, ko atishawa, to, dole ne su sanya marufin hanci da baki nan da nan, su kuma je ganin likita kan lokaci, su kuma kebe kansu daga jariransu. Sa’an nan kuma, idan har haka ya faru, to, bai kamata iyayen su sunbaci jariransu ba, kada su yi tari, ko yin arishawa ko numfashi a gaban fuskar jariransu. Kamata ya yi su rufe baki da hanci da takardar goge baki ko kuma gwiwar hannu, a kokarin kare jariran daga kamuwa da kwayoyin cuta.

A zaman rayuwar yau da kullum dole ne iyayen su fito da kyakkyawar al’adar cin abinci, alal misali, su kaucewa taba ko sanyaya abincin da jariran suke ci da baki, musamman ma tauna abincin sa’an nan su baiwa jariran su ci, kada su yi amfani da kayayyakin cin abinci tare da jariran. Ban da haka kuma, ya kamata a rika tsabtace, tare da kashe kwayoyin cuta a jikin kayayyakin cin abinci da abubuwan wasa a lokaci-lokaci. Kada su je gangami ko cin abinci tare da wasu mutane tare da jariran da kananan yara. Ya fi kyau a tabbatar da jarirai da kananan yara sun yi wasa a fili, inda babu mutane masu yawa. Dole ne a ba da tazara yayin mu'amala da juna, da shigar da iska mai damshi cikin daki lokaci-lokaci. Wajibi ne a tabbatar da kananan yara sun ci abinci yadda ya kamata. Wani abu mai muhimmanci shi ne, a yi wa kananan yara da jarirai allura kan lokaci. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan