logo

HAUSA

Shugaban cibiyar nazarin harkokin kiwon lafiya ta Amurka: “cutar COVID-19 ta samo asali daga dakin gwaje-gwaje na Wuhan” karya ce

2021-06-05 21:47:53 CRI

Shugaban cibiyar nazarin harkokin kiwon lafiya ta Amurka: “cutar COVID-19 ta samo asali daga dakin gwaje-gwaje na Wuhan” karya ce_fororder_微信图片_20210605211137

Rahotanni daga jaridar New York Post sun ce, a cikin wani sakon imel da aka wallafa kwanan nan, an bayyana cewa, shugaban cibiyar nazarin harkokin kiwon lafiya ta Amurka Francis Collins ya karyata jita-jitar da ake yadawa wai kwayar cutar COVID-19 ta samo asali daga dakin gwaje-gwaje na birnin Wuhan na kasar Sin, inda a cewarsa, karya ce zalla babu gaskiya ko kadan.

Shugaban cibiyar nazarin harkokin kiwon lafiya ta Amurka: “cutar COVID-19 ta samo asali daga dakin gwaje-gwaje na Wuhan” karya ce_fororder_微信图片_20210605211142

Rahotannin sun ce, a ranar 18 ga watan Afrilun bara, daya daga cikin kwararrun WHO da suka je kasar Sin don binciken asalin kwayar cutar, Mista Peter Daszak ya rubutawa Anthony Fauci sakon imel, inda ya gode masa saboda ya fito fili don shaida cewa, jemagu ne suka baza kwayar cutar COVID-19 zuwa ga dan Adam, amma ba wai daga dakin gwaje-gwajen Wuhan ba.

Peter Daszak ya kuma ce, Fauci jarumi ne, kuma kalamansa za su taimaka ga kawar da shaci-fadin dake cewa wai asalin cutar shi ne birnin Wuhan na kasar Sin. (Murtala Zhang)