logo

HAUSA

WHO: Karin yaduwar COVID-19 a Afirka na barazana ga tsarin kiwon lafiyar nahiyar

2021-06-04 09:39:11 CRI

Daraktar shiyyar Afirka a hukumar lafiya ta duniya WHO Matshidiso Moeti, ta ce rahotanni na nuna yadda a baya bayan nan ake samun karuwar masu harbuwa da cutar numfashi ta COVID-19 a sassan nahiyar Afirka, a gabar da ake sassauta dokokin kulle, da kuma sanyayar yanayi a wasu bangarorin nahiyar. Baya ga batun karancin rigakafin da ake bukata, domin yiwa mafiya fuskantar hadarin harbuwa da cutar.

Jami’ar ta ce, wannan yanayi na matukar barazana ga tsarin kiwon lafiyar Afirka wanda da ma ke da rauni. Moeti ta yi gargadin cewa, karatowar yanayin hunturu na iya bunkasa yaduwar cutar a sassan Afirka, don haka ya zama wajibi gwamnatoci su habaka samar da ababen bukata na yaki da annobar don kaucewa mummunan tasirin ta.

Alkaluman WHO sun nuna cewa, Afirka ta samu karin kaso 20 bisa dari na masu harbuwa da cutar COVID-19 cikin makwanni 2 da suka gabata, yayin da kasashen nahiyar 8 suka samu karin kaso 30 bisa dari cikin mako guda.  (Saminu)