logo

HAUSA

Sin da Afghanistan da Pakistan sun cimma matsayar bunkasa zaman lafiya da yaki da ta’addanci a Afghanistan

2021-06-04 16:34:08 CRI

Sin da Afghanistan da Pakistan sun cimma matsayar bunkasa zaman lafiya da yaki da ta’addanci a Afghanistan_fororder_0604Saminu4Afghanistan

Babban dan majalissar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya jagoranci zama na 4, na tattaunawa game da al’amuran da suka jibanci kasashen uku.

Ministan harkokin wajen Afghanistan Mohammad Haneef Atmar, da takwaransa na Pakistan Shah Mahmood Qureshi, sun halarci taron na jiya Alhamis da aka shirya daga birnin Guiyang na kasar Sin ta kafar bidiyo.

Manyan jami’an uku, sun amince da aiwatar da matakan wanzar da zaman lafiya da sulhu a Afghanistan, tare da karfafa hadin gwiwar sassan uku. Kaza lika sun amince da ci gaba da lalubo dabarun zurfafa hadin kai, don shawo kan kalubalen bazuwar cutar COVID-19.

Har ila yau, sun yarda da bukatar fadada hadin gwiwar aiwatar da shawarar “zira daya da hanya daya” a Afghanistan, ta yadda hakan zai amfani daukacin al’ummun yankin da kasar take. Kana sun jaddada burin su na yaki da dukkanin wasu nau’o’in ayyukan ta’addanci.

A hannu guda kuma, ministocin kasashen uku, su bukaci karfafa yaki da kungiyar masu tsattsauran ra’ayin Islama ta “East Turkistan” da sauran kungiyoyi makamantan ta, ta yadda za a kai ga cimma burin wanzar da tsaro da daidaito a yankin.

Bugu da kari, Sin da Pakistan sun sake jaddada goyon bayansu, ga manufar dawo da zaman lafiya, da sake gina Afghanistan, tare da fatan su na fadada musaya a fannonin tattalin arziki da cikikayya da Afghanistan, da ma taimakawa kasar wajen rayawa da dogaro da kai.

Yayin zaman, ministocin harkokin wajen Afghanistan da Pakistan, sun nuna aniyarsu ta karfafa musayar ra’ayoyi da tsare-tsare, da zurfafa fahimtar juna ta fuskar amincewar juna, tare da kago dabarun wanzar da zaman lafiya da ci gaban hadin gwiwar su.    (Saminu)