logo

HAUSA

An gudanar da riga-kafin COVID-19 sama da miliyan 700 a fadin kasar Sin

2021-06-04 11:24:14 CRI

An gudanar da riga-kafin COVID-19 sama da miliyan 700 a fadin kasar Sin_fororder_0604Ahmad4-allura

Hukumar lafiyar kasar Sin ta bayyana cewa, ya zuwa ranar Laraba, an gudanar da riga-kafin COVID-19 sama da miliyan 704.8 a duk fadin kasar.

Jimillar nau’in riga-kafi 20 ne suka shiga dakin gwaji a kasar Sin tun daga shekarar da ta gabata, kamar yadda Zheng Zhongwei, jami’in hukumar lafiyar kasar NHC ya bayyana. Kasar Sin tana sahun gaba a duniya ta fuskar adadin yawan nau’ikan riga-kafin da ake samarwa.

Yayin da kasar ke gaggauta gudanar da riga-kafin a cikin gida da kuma yin bincike da nazarin samar da riga-kafin, kasar Sin tana kuma yin bakin kokarinta wajen taimakawa al’ummar duniya wajen samun riga-kafin na COVID-19, duk da yawan al’ummar da take da shi da karancin riga-kafin a cikin gida.

Kawo yanzu, ta samar da riga-kafin COVID-19 sama da miliyan 350 ga al’ummomin kasashen duniya, wanda ya hada har da taimakon riga-kafin da ta samarwa kasashe maso tasowa sama da kasashe 80 da kuma fitar da riga-kafin zuwa wasu kasashe sama da 40, wanda hakan ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen samar da riga-kafin a duniya.

Riga-kafin COVID-19 na kamfanin Sinovac shi ne riga-kafi na biyu daga kasar Sin da hukumar lafiya ta duniya WHO ta amince a yi amfani da shi don bukatun gaggawa, bayan na kamfanin Sinopharm, wanda aka sabunta amfani da shi tun a watan da ya gabata.

Sabuntawar da aka yi, ya nuna kwakkwarar hujja dake nuna cewa riga-kafin na kasar Sin dukkansu suna da kyau da kuma inganci, kana za su ba da gagarumar gudunmawa wajen cike gibin da ake da shi tare da kawar da rashin daidaito a tsarin samarwa da rarraba riga-kafin a duniya.

Kasar Sin ta kuma ayyana goyon bayanta na kawar da dokar hakkin mallakar fasahar riga-kafin COVID-19, kana tana goyon bayan kungiyar kasuwanci ta duniya da sauran hukumomin kasa da kasa wajen zartas da kudurori dake shafar wannan batu.

Kasar Sin ta kuma gabatar da aniyar shirya taron dandalin kasa da kasa game da hadin gwiwa a fannin riga-kafin domin lalibo hanyoyin da za a bi don tabbatar da yin adalci a tsarin rarraba riga-kafin a duniya. (Ahmad)