logo

HAUSA

Amurka za ta haifarwa kan ta da illa ta hanyar shigar da CIA harkar binciken asalin COVID-19

2021-06-04 17:32:07 CRI

Amurka za ta haifarwa kan ta da illa ta hanyar shigar da CIA harkar binciken asalin COVID-19_fororder_210604-Amurka-Jamus

Rahotannin baya bayan nan na cewa gwamnatin Amurka, ta mika ragamar binciken asalin cutar COVID-19 ga hukumar leken asirin kasar CIA, wanda hakan ke nuni da cewa, Amurka ta maida batun wannan bincike harkar da ta shafi CIA.

To sai kuma, masharhanta da dama na ganin binciken asalin kwayar cutar harka ce ta kimiyya tsantsa, ba ta wata hukumar leken asiri ba, kuma ya dace a bi hanyar adalci, ba ta kokarin shafawa wani bangare kashin kaji ba, kana a yi hadin gwiwar cimma nasara ba wai yin fito na fito ba.

Ko shakka ba bu, umarnin da fadar shugaban Amurka ta bayar ga CIA na ta shiga bincike kan asalin kwayar cutar, na nuna aniyar Amurka a fili na siyasantar da aikin, wanda kuma tabbas zai illata kokarin da ake yi na hadin kan kasa da kasa, a aikin zakulo asalin COVID-19, kuma matakin na Amurka ya cancanci a bincike shi.   (Saminu)