logo

HAUSA

Masanin Rasha: Kasashen yamma na danganta bullar COVID-19 da dakin gwaji domin cimma burin siyasa

2021-06-04 11:12:02 CRI

Masanin Rasha: Kasashen yamma na danganta bullar COVID-19 da dakin gwaji domin cimma burin siyasa_fororder_病毒-1

Wani masani dan kasar Rasha Mikhail Morozov, ya wallafa makala a wata kafar watsa labaran kasar, inda a ciki ya zargi wasu tsirarun kasashen yammacin duniya, da kokarin dorawa kasar Sin alhakin bazuwar cutar numfashi ta COVID-19, bisa burin su na yiwa al’ummar duniya rufa rufa, da cimma burikan siyasa.

Makalar ta nuna cewa, Birtaniya da Amurka da wasu kasashe kawayen su, sun sha zargin kasar Sin da yada wannan cuta, suna masu cewa mutum ne ya kirkiri cutar. Game da hakan, Morozov ya ce tun da wadannan kasashe na zargin mutum ne ya kirkiri cutar, to kamata ya yi a yi cikakken bincike kan hakan.

Ya ce baya ga birnin Wuhan, ya dace kuma tawagar kwararrun hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ziyarci cibiyar Fort Detrick dake sansanin sojojin Amurka, da cibiyoyin gwaje gwajen kwayoyin cututtuka da ake amfani da su a yaki, dake sassan kasashen duniya daban daban, domin tantance dukkanin wani zargi.  (Saminu)