logo

HAUSA

Ghana ta fara zagaye na biyu na riga-kafin COVID-19

2021-05-20 10:02:33 CRI

Ghana ta fara zagaye na biyu na riga-kafin COVID-19_fororder_210520-Ghana

A jiya Laraba kasar Ghana ta kaddamar da fara zagaye na biyu na aikin riga-kafin cutar COVID-19 a cibiyoyin riga-kafi 43 da aka kebe a fadin kasar.

Ana sa ran jami’an lafiyar kasar zasu yiwa jama’a riga-kafin kimanin allurai 350,000 na kamfanin AstraZeneca wadanda aka kai zuwa kasar Ghana karkashin yarjejeniyar COVAX.

Kasar ta yammaci Afrika itace ta farko da ta karbi riga-kafi daga hukumar lafiya ta duniya WHO karkashin shirin COVAX a watan Fabrairu kuma ta fara aikin riga-kafin a farkon watan Maris. (Ahmad)