logo

HAUSA

An nada Yeboah na Ghana mataimakin shugaban kwamitin da’a na FIFA

2021-05-23 17:26:16 CRI

An nada babban mai shari’a na kasar Ghana Anin Yeboah, mukamin mataimakin shugaban kwamitin da’a na hukumar shirya wasan kwallon kafa ta kasa da kasa FIFA, wanda hukumar gudanarwar kwallon kafan duniyar ta amince da nadin.

Yeboah, ana fatan zai yi aiki tare da shugaban kwamitin Jorge Palacio domin kula da dukkan batutuwa dake shafar da’a game da hukumar kwallon kafan duniyar na tsawon shekara guda.

Dama dai babban mai shari’ar na kasar Ghana ba bako ba ne a fagen wasannin kwallon kafa, kasancewar shi mamba ne a kwamitin shari’ar hukumar ta FIFA, kuma shi ne ke rike da shugabancin kwamitin da’ar tun a watan Mayun shekarar 2017 da aka zaba a taron FIFA karo 67 a Bahrain.

Ya kuma kasance shugaban kwamitin dokokin FIFA, kana an bayyana shi a matsayin jami’in aiwatar da sauye sauye na tawagar hadin gwiwa ta hukumar shirya wasan kwallon kafan Afrika da na hukumar kwallon kafan kasa da kasa CAF/FIFA a watan Satumbar 2019.(Ahmad)