logo

HAUSA

Ghana za ta fara zagaye na biyu na rigakafin COVID-19

2021-05-17 10:43:06 CRI

Ghana za ta fara zagaye na biyu na rigakafin COVID-19_fororder_加纳总统-Nana Addo Dankwa Akufo-Addo

A ranar Laraba kasar Ghana za ta fara zagaye na biyu na aikin rigakafin cutar COVID-19, shugaban kasar Ghanan Nana Addo Dankwa Akufo-Addo ya bayyana hakan.

A jawabin shugaban ga ‘yan kasar game da yaki da cutar COVID-19 a karo na 25, ya ce, fara aikin rigakafin zagaye na biyu ya biyo bayan karbar karin allurai kimanin 350,000 na kamfanin AstraZeneca karkashin yarjejeniyar COVAX.

Shugaba Akufo-Addo ya ce, wannan adadin alluran kari ne a kan wadanda ake da su domin yiwa mutane 360,000 daga gundumomin kasar 43 zagaye na biyu na rigakafin, wadanda suka karbi kashin farko na alluran tsakanin ranar 1 zuwa 9 ga watan Maris.

Ya ce, Ghana tana sa ran wasu alluran kimanin 300,000 na kamfanin Sputnik V wadanda tuni hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasar Ghana ta amince da su domin inganta aikin rigakafin a kasar.

Shugaban na Ghana ya ce, za a yi kokarin tabbatar da yiwa mutanen da suka karbi alluran a zagayen farko bayan ranar 9 ga watan Maris, za a tabbatar sun karbi rigakafin zagaye na biyu a kan lokacin da ya dace.

Ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da daukar matakan takaita zirga-zirgar jama’a har zuwa lokacin da kasar za ta samu cikakkiyar garkuwa domin jama’a su samu damar komawa harkokinsu na yau da kullum.(Ahmad)