logo

HAUSA

Shugaba Xi Jinping ya zanta da shugaban Iran ta wayar tarho

2021-05-24 21:00:43 CRI

A yau Litinin ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya zanta da shugaban Iran Hassan Rouhani ta wayar tarho. Yayin da suke tattaunawa, shugaba Xi ya ce a bana ake cika shekaru 50 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Iran. Kuma Sin a shirye take ta ci gaba da aiki tare da Iran din, wajen kara karfafa hadin gwiwarsu a sassa daban daban, da karfafa ci gaban hadin gwiwar su bisa matsayin koli daga dukkanin fannoni.

A nasa bangare shugaba Rouhani, bayyana fata ya yi, na ganin kasar sa ta ci gaba da cudanya da kasar Sin, tare da adawa da ware kai, da yin babakere, tare da fatan wanzar da zaman lafiya da tsaron shiyyar da suke.

A dai wannan rana, shugaban na Sin ya kuma zanta da takwaransa na Vietnam Nguyễn Xuân Phúc.   (Saminu)