logo

HAUSA

Xi Jinping ya bukaci da a karfafa ci gaban kasa ta hanyar kimiyya da Fasaha

2021-05-28 19:41:55 CRI

Xi Jinping ya bukaci da a karfafa ci gaban kasa ta hanyar kimiyya da Fasaha_fororder_习近平-3

A yau Juma’a ne aka gudanar da babban taron masanan cibiyar kimiyya, da ayyukan injiniya, da kuma taro na 10, na gamayyar kungiyoyin raya ayyukan masana kimiyya na Sin, a nan birnin Beijing.

Cikin muhimmin jawabin da ya gabatar yayin taron, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada muhimmancin amfani da kimiyya da fasaha, a matsayin jigon raya kasa, da bunkasa ci gaba mai inganci, wanda kuma zai share fagen aiwatar da matakan farfado da kasa, karkashin inuwar ilimin kimiyya.

Kaza lika hakan a cewar sa, zai karfafa ci gaban kasar Sin, ta hanyar zakulo masu basira a fannoni daban daban, da bunkasa aniyar kasa a fannin raya kirkire kirkire, da ingiza kafa kasa mai karfin gaske a fannin kimiyya da fasaha, da cimma matakin dogaro da kai na kasa, a matakin koli.  (Saminu)