logo

HAUSA

Xi Ya Yi Wa Babban Taron Kolin Lafiyar Duniya Jawabi

2021-05-21 21:19:31 CRI

A yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya halarci taron kolin lafiya na kasa da kasa, tare da gabatar da jawabi ta kafar bidiyo daga nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

A jawabin nasa, shugaba Xi ya ce, yaki da annobar COVID-19, na mutane ne, wanda kuma mutane za su yi. A don haka ya yi kira da a kara kokari, wajen martaba kima da darajar dukkan ran bil-Adama.

Shugaban na Sin ya kuma yi kira ga kasashen duniya, da su martaba kimiyya, da amfani da matakai da dokoki na kimiyya, yayin da duniya ke fama da sabbin nau’o’in cutar COVID-19.

Ya ce, sanya batun siyasa ba zai taimakawa matakan yaki da annobar ba, sai ma ya wargaza hadin gwiwar kasa da kasa game da yaki da kwayar cutar, da kawo babbar illa ga jama’a a duniya baki daya.

Xi Jinping ya bayyana cewa, annobar COVID-19, wata babbar jarrabawa ce ga tsarin kiwon lafiyar duniya, a don haka ya yi kira da a inganta matakan kandagarki da dakile yaduwar cututtuka. Ya kuma bukaci daukar matakai, don kara karfi a fannoni guda biyar. Na farko, sanya ido, da gargadin farko da daukar matakan gaggawa. Na biyu, jinyar manyan annoba, Na uku, tanadin ko-ta-kwana da tsare-tsare. Na hudu, yaki da bayanan karya, sai na biyar, samar da taimako ga kasashe masu tasowa.

A cikin jawabinsa, shugaba Xi Jinping ya yi nuni da cewa, Sin ta samar da gudummawar da darajarta ta kai dalar Amurka biliyan 2 don taimakawa kasashe masu tasowa da suke fama da yaduwar cutar COVID-19, ta yadda za su yi yaki da cutar da farfado da tattalin arziki da zamantakewar al’umma. Sin ta samar da gudummawar kayayyaki ga kasashe fiye da 150 da kungiyoyin kasa da kasa 13, da samar da abin rufe baki da hanci fiye da biliyan 280 da rigunan kariya fiye da biliyan 3 da miliyan 400 da kuma kayayyakin binciken kamuwa da cutar fiye da biliyan 4 ga dukkan duniya. An kafa tsarin hadin gwiwar asibitoci 41 a tsakanin Sin da Afirka, kana an fara gina babban ginin cibiyar yaki da cututtuka ta Afirka da Sin ta taimaka wajen ginawa a karshen shekarar bara. Sin ta aiwatar da yarjejeniyar sassauta biyan basusukan da ake bin kasashe masu fama da talauci da kungiyar G20 ta tsara, yawan kudin basusukan da Sin ta sassauta su biya ya kai dala biliyan 1.3, Sin ta kasance kasar da ta fi sassautawa kasashe mafi talauci biyan basusukanta a cikin kasashe membobin kungiyar G20.

A kokarin ganin an ci gaba da nuna goyon baya ga yaki da cutar COVID-19 ta hanyar hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa, Xi Jinping ya sanar da cewa, Sin za ta kara samar da gudummawa da darajarsu ta kai dala biliyan 3 a cikin shekaru 3 masu zuwa, don nuna goyon baya ga kasashe masu tasowa wajen yaki da cutar COVID-19 da farfado da tattalin arziki da zamantakewar al’umma. Sin ta riga ta samar da alluran rigakafin cutar miliyan 300 ga dukkan duniya, ta kuma yi kokarin samar da alluran ga kasashen waje. Sin ta bukaci kamfanoninta da su yi musayar fasahohi ga kasashe masu tasowa, da yin hadin gwiwa wajen samar da rigakafin tare. Kana Sin ta riga ta amince da kawar da sharadin ‘yancin mallakar fasahar riga kafin COVID-19, da nuna goyon baya ga kungiyoyin kasa da kasa kamar WTO da su tsara kuduri game da wannan batu. Hakazalika, Sin ta yi kira da a kafa dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar samar da alluran rigakafin cutar, inda kasashe masu nazarin samar da alluran rigakafin cutar, da kamfanonin dake samar da su, da bangarorin da abin ya shafa, za su tattauna tare kan yadda za a rarraba alluran rigakafin cutar a duniya cikin adalci. (Ibrahim & Zainab)

Ibrahim & Zainab